An jefa yarinya a rijiya bayan yi mata fyaɗe

Matashin ya yi yarinyar wannana aika-aika ne bayan ya yi arba da ita a lokacin da mahaifiyar ta aike ta a Rukunin Gidajen Jakadu da ke garin Katsina.

An jefa yarinya a rijiya bayan yi mata fyaɗe

Kotu

Wani saurayi ɗan shekara 24 ya shiga hannu kan zargin jefa wata budurwa ’yar shekara 17 a rijiya bayan ya yi mata fyaɗe a Jihar Katsina.

Matashin ya yi yarinyar wannana aika-aika ne bayan ya yi arba da ita a lokacin da mahaifiyar ta aike ta a Rukunin Gidajen Jakadu da ke garin Katsina.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce wanda ake zargin ya yi wa yarinyar barazana ne da wata sharɓeɓiyar wuka, inta ya tisa keyarta zuwa wani kango ya keta huruminta da karfin tuwo.

Bayan ya kamamal kuma a kokarinsa na ɓatar da sahun abin da ya aikata ne ya jefa ta a cikin wata rijiya ya kuma jefa duwatsu a ciki a a ranar 27 ga watan Satumba.

Duk da haka, Allah Ya yi mata gyaɗar dogo, inda daga bisani ’yan sanda suka ceto ta taga rijiyar, bayan gudanr da bincike kuma suka cika hannu da wanda ake zargin.

Tags