An jefe wani saurayi a Somaliya
A ranar Talatar da ta gabata ne aka jefe wani saurayi har lahira a yankin kudancin kasar Somaliya bayan wata kotun shari’ar Musulunci ta same shi da laifin yi wa wata mata fyade. Alkalin kotun ya ba da matashin mai suna Hassan Ahmad Ali, dan kimanin shekara 18, da ya biya yarinyar diyyar da dan […]
A ranar Talatar da ta gabata ne aka jefe wani saurayi har lahira a yankin kudancin kasar Somaliya bayan wata kotun shari’ar Musulunci ta same shi da laifin yi wa wata mata fyade.
Alkalin kotun ya ba da matashin mai suna Hassan Ahmad Ali, dan kimanin shekara 18, da ya biya yarinyar diyyar da dan maraki kafin kisansa kamar yadda wani faifan da aka nadi zaman kotun ya bayyana. Kodayake, saurayin ya musanta tuhumar kuma yake da amincewar hakan ya faru.
Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce matashin ya yi wa yarinyar fyade ne bayan da ya yi mata barazanar kisa da bindigar da yake rike da ita.
A watan jiya ma, kungiyar al-Shabab ta jefe wata mata bayan ta same ta da laifin yin zina a garin Barawe bayan ta auri maza hudu lokaci guda.
A baya-bayan nan, al-Shabab ta rasa iko da garuruwa da dama, ciki har da Barawe, amma har yanzu tana da iko da manyan yankunan karkarar kasar.
kungiyar al-Shabab wadda take da alaka da kungiyar al-kaeda, tana da mayaka akalla 5,000. Kuma tana gwagwarmayar hanbarar da gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan Majalisar dinkin Duniya.