An jefi Alhaji Sule Lamido a Hadeja
A ranar Litinin da ta gabata wadansu matasa sun jefi ayarin tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido tare da yi masa ihu barawo a lokacin da ya ziyarci garin Hadeja da ke jihar.An ce matasan sun yi wa Alhaji Sule Lamido ihu ne suna jifar tawagarsa saboda zargin cewa a lokacin mulkinsa na shekara […]
A ranar Litinin da ta gabata wadansu matasa sun jefi ayarin tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido tare da yi masa ihu barawo a lokacin da ya ziyarci garin Hadeja da ke jihar.
An ce matasan sun yi wa Alhaji Sule Lamido ihu ne suna jifar tawagarsa saboda zargin cewa a lokacin mulkinsa na shekara takwas bai tsinana wa jama’ar Hadeja komai ba.
Matasan sun kunyata tsohon Gwamnan ne tun daga fadar Mai martaba Sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubakau Maje, inda matasan suka sa motocinsa a gaba suna ihu barawo har wajen gari.
Majiyarmu ta ce matasan sun farfasa motocin da ke cikin ayarin tsohon Gwamnan, suna cewa “barawo ka dawo mana da kudinmu da ka sace da barawo ba ma yi, ba ma yi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, DSP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce amma saboda suna taro da shugabanninsa ba zai yi dogon bayani ba sai bayan sun gama.