An jefi Sarkin Kano a filin rantsar da Abba Gida-Gida

An rika jifan Sarakunan da ‘fiya wata’.

An jefi Sarkin Kano a filin rantsar da Abba Gida-Gida

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka magoya bayan jam’iyyar NNPP na yi wa Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da takwaransa na Bichi, Nasiru Ado Bayero ihu a filin rantsar da sabuwar Gwamnatin Kano.

Haka kuma, Sarakunan sun sha jifa da ruwan leda da aka fi sani da ‘fiya wata’ yayin da jami’an tsaro suka yi musu kawanya har zuwa wurin zamansu a harabar filin rantsar da sabon Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, da zuwan Sarakunan ne aka soma tarbarsu da ihu da ke nuna alamar ‘bama yi’ a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Dabo.

Aminiya ta samu cewa wasu daga cikin magoya bayan Zababben Gwamnan sun rika jifan Sarakunan da ruwan leda hadi da robobin lemu.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara