An jibge jami’an tsaro 40,000 albarkacin zaben gwamna a Kogi

Muna shirye da duk wasu masu tayar da zaune tsaye da ke shirin kawo cikas a lokacin zaben.

An jibge jami’an tsaro 40,000 albarkacin zaben gwamna a Kogi

‘Yan sanda

Kimanin jami’an tsaro dubu 40 ne aka jibge a Jihar Kogi domin tabbatar da an gudanar da zaben gwamnan jihar lafiya da za a yi a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Hukumomin tsaron dai sun sha alwashin tabbatar da tsaro a lokacin wannan zabe wanda ga bisa dukkan alamu yake cike da kalubale da kuma fargaba.

Zaben na jihar Kogi za a gudanar da shi ne tare da na jihohin Imo da Bayelsa da ke Kudancin kasar.

Jami’an tsaron da aka tura Kogin sun hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma Civil Defence da ma sauran masu damara tuni suka mamaye lungu da sako na Jihar Kogin

Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda, DIG Habu Sani daga Hedikwatar rundunar ‘yan sandan  aka aika jihar ta Kogi domin tabbatar da zaben ya gudana lafiya.

DIG Sani ya kuma ce suna shirye da duk wasu masu tayar da zaune tsaye da ke shirin kawo cikas a lokacin zaben.

A halin da ake ciki dai Gwamna Yahaya Bello ya bukacin rundunar ‘yan sandan Najeriyar da ta gudanar da kwakkwaran bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikice-rikicen da suka auku lokacin yakin neman wannan zabe na ranar Asabar.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa