An jikkata jami’an kwastam, shugaban karamar hukama ya tsallake rijiya da baya

Wani gungun matasa ’yan sumoga daga garuruwan Igbeti da Kishi a Jihar Oyo da hadin guiwar abokansu daga Ilorin a Jihar Kwara, dauke da makamai, sun yi wa jami’an kwastam jina-jina, suka lalata motocinsu a Igbeti da ke kan iyakar Najeriya da Jumhuriyar Benin, a ranar Talatar makon jiya, a lokacin da suka yi wani […]

An jikkata jami’an kwastam, shugaban karamar hukama ya tsallake rijiya da baya
An jikkata jami’an kwastam, shugaban karamar hukama ya tsallake rijiya da baya

Wani gungun matasa ’yan sumoga daga garuruwan Igbeti da Kishi a Jihar Oyo da hadin guiwar abokansu daga Ilorin a Jihar Kwara, dauke da makamai, sun yi wa jami’an kwastam jina-jina, suka lalata motocinsu a Igbeti da ke kan iyakar Najeriya da Jumhuriyar Benin, a ranar Talatar makon jiya, a lokacin da suka yi wani kwanton bauna a cikin daji suka kwace manyan motoci dauke da kayan da aka haramta shigowa da su daga hannun jami’an kwastam da suka kama kayan.
Shi kuma Shugaban karamar Hukumar Olorunsogbo, Mista Wasiu Adekunle Olatunbosun ya tsallake rijiya da baya daga hannun wadannan ’yan sumoga da suka yi kokarin cin zarafinsa, saboda shawarar hana su yanke wa kansu hukumci da kyale jami’an kwastam su gudanar da aikinsu domin girmama doka da oda ba ta shiga kunnensu ba.
Da yake wa ’yan jarida bayani a Ibadan, a ranar Juma’a dangane da irin barnar da aka yi, Kodineta kuma Kwamandan Runduna ta musamman a kan Yaki da ayyukan fasa kwauri, Mataimakin Kwanturola Hassan Shallangwa ya ce tawagar tashi daga Abuja, ta kai ziyarar gani-da-ido ne zuwa garin Igbeti, ya nuna alhininsa da wannan aika-aika da matasan suka yi. “Shugaban karamar Hukumar Olorunsogbo da dattijan gari da sauran masu fada-a-ji sun cancanci yabo saboda kokarinsu dangane da ayyukanmu da suke ba mu hadin kai da goyon baya. Rundunar ta musamman, ta toshe hanyoyin Baba Eko da Bani na tsawon mako 3 domin hana masu fasa kwaurin yin amfani da hanyoyin. daukar wannan mataki da muka yi, ya sa sun kasa samun hanyar da motocinsu dauke da buhunan shinkafa za su iya wucewa, sai suka sauya akala suke tafiya cikin daji a kasa domin shiga cikin gari. A daidai wannan lokaci ne wasu motoci dauke da buhunan shinkafa suka yi jerin gwano domin wucewa ta kan wannan hanya, wanda jami’anmu suka yi kokarin hana su, amma suka yi amfani da yawansu suka auka mana, sai mota guda daya tak muka kama, suka raunata jami’anmu, suka lalata motocinmu guda 3. daya daga cikin jami’an mai suna Idotade Jelili Alani, ya samu munanan raunuka, kuma suna kwance a asibiti tare da sauran abokan aikinsa. Mun kama ’yan sumoga mutum 5 wadanda za mu gabatar da su gaban kuliya bayan mun kammala bincike”.
A nan, sai Hassan Shallangwa ya nemi jama’a, musamman wadanda suke zaune a kusa da kan iyakokin kasa, su taimaka wajen hanzarta bayar da labari ga jami’an kwastam domin dakile miyagun ayyukan da masu fasa kwauri ke haifarwa ga kasa. Ya ce sashen runduna ta musamman a kan yaki da fasa kwauri yana da jami’ai da suka samu horo da gogewa a kan ayyukansu, wanda hakan ne ya sa suke samun nasara.
Dangane da nasarorin da suka samu sai ya ce, a cikin watanni 6, rundunar ta musamman ta yi nasarar yin kame har sau 105 na irin kayan da aka haramta shigowa dasu cikin kasa da ya kamata a biya musu harajin Naira miliyan 99 da dubu dari 8 domin shigowa da su cikin kasa ta halattacciyar hanya, kuma an kama mutum 6 da aka durkusar da su gaban kotu.