An jikkata mutane da dama a rikicin makiyaya da manoma a Kano

Rikicin ya fara ne lokacin da aka zargi makiyaya da cin amfanin gona a yankin

An jikkata mutane da dama a rikicin makiyaya da manoma a Kano

Masu Rikici

Mutane da dama ne aka rawaito sun jikkata sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a garuruwan Dusai da ’Yan Gamji na Karamar Hukumar Dambatta a Jihar Kano.

Aminiya ta rawaito cewa rikicin ya auku ne ranar Alhamis a lokacin da wasu makiyaya da aka yi zargin sun far wa manoma da ke tsaka da aiki a gonarsu inda suka harbe su da kibiya tare da sarar su da adda da sauran munanan makamai.

Wani mazaunin garin mai suna Baffa Dambatta, ya shaida mana cewa wasu makiyaya sun dauki makamai sun far wa wasu manoma a lokacin da suke aiki a gonarsu lamarin da ya janyo aka bar mutane kwance cikin jini.

Ya ce, “Mutumin da suka fara far wa yana aiki a gonarsa sai makiyayan suka tura shanunsu suka fara ci masa amfanin gona.

“Hakan ta sa ya je ya same su don yi musu magana. Amma a maimakon su ba shi hakuri sai suka biyo shi suna harbin sa da kibiya, suna saran shi da adda.

“An dauki mutunen da aka raunata din zuwa Babban Asibitin Dambatta kafin daga bisani a mayar da su Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano don samun kulawar likitoci,” in ji Baffa Dambatta.

Daya daga cikin mutanen da suka jikkata da suke karbar magani a asibiti ya bayyana cewa makiyayan sun far masa ne a lokacin da yake aiki a gonarsa.

“A duk lokacin da muka yi girbi sai mutanen nan su zo da shanunsu su lalata mana amfanin gona. Yaya za mu zura ido mu kyale irin wannan abu ya ci gaba da faruwa. Hakan ya sa a wannan lokacin da suka yi mana sai muka je muka yi musu magana amma sai suka biyo mu da kwari da baka suna harbin mu. Wallahi ni kaina sai da aka cire min kibiya a bayana.” in ji wani da lamarin ya shafa da ya nemi a sakaya sunansa.

Wani da ’ya’yansa biyu suka jikkata a rikicin ya bayyana cewa yana gida aka kira shi aka aka fada masa cewa makiyaya sun far wa ’ya’yansa, yana zuwa ya same su cikin jini da kibiya a soke a jikinsu.

“An fada min cewa makiyaya ne suka kai wa ’ya’yana hari. Wannan abin da suke yi ba yau suka fara ba. Idan mun yi noma su rika zuwa gonakinmu su na yi mana barna. Mun kai kara ga ’yan sanda amma ba a share mana hawaye ba.

Malam Yusha’u Galadima shi ne Dagacin garin ’Yan Gamji, ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da rikicin ya barke, mai unguwar Dusai ya kira ’yan sanda amma ba su yi wani abu a kan lokaci ba.

Mazauna garuruwan dai nemi gwamnati da ta yi duk mai yiyuwa don shawo kan lamarin kafin abubuwan su kai ga lalacewa.

Tuni dai harkoki suka koma daidai a garuruwan na Dusai da ’Yan Gamji, inda mutane suka koma bakin aikinsu .

Sai dai duk kokarinmu don jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura sakamakon bai amsa kiran da aka yi ta yi a wayarsa ba.

Haka kuma bai bayar da amsar sakon kar-ta-kwanan da muka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.