An jingine mata gefe a siyasar kasar nan – A’isha Maijama’a
Hajiya A’isha Yakubu Maijama’a fitacciyar ’yar siyasa ce a Jihar Kano kuma ’yar Jam’iyyar PDP. Ta taba zama Mashawarciyar Gwamna kuma tsouwar Shugabar Mata ta Jam’iyyar ANPP, kuma har ila yau ta yi takarar Majalisar Wakilai a ANPP, kuma ta zama Daraktar Yakin Neman Zaben dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar ANPP Malam Salihu […]
Hajiya A’isha Yakubu Maijama’a fitacciyar ’yar siyasa ce a Jihar Kano kuma ’yar Jam’iyyar PDP. Ta taba zama Mashawarciyar Gwamna kuma tsouwar Shugabar Mata ta Jam’iyyar ANPP, kuma har ila yau ta yi takarar Majalisar Wakilai a ANPP, kuma ta zama Daraktar Yakin Neman Zaben dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar ANPP Malam Salihu Sagir Takai. A tattaunawarta da Aminiya ta ce mata suna fuskantar wariya a tafiyar siyasar kasar nan, don haka ta yi kira da a ba mata damar tsayawa takara ba kawai su fito su yi zabe ba da sauran batutuwa da suka shafi siyasar:
A kwanakin nan ne aka yi bikin Ranar Mata ta Duniya, yaya za ki bayyana ci gaban da matan suka samu musamman a shekarun baya-bayan nan?
To alhamdulillahi za mu iya cewa mata suna samun ci gaba a harkar ilimi da sana’a da sauransu domin ko’ina ka leka za ka ga mata ba kamar shekarun baya ba. Zan iya cewa a bangaren siyasa ne kawai ake tauye mata domin an hana su su fito su yi takara a zabe su su rike mukamai sai dai kullum a nada su. Sau biyu ina tsayawa takara amma ban samu ba. Kin san yadda siyasar Kano take, ba a ba mace dama ta gwada tun daga zaben cikin gida za a kayar da ke ba za ma a bari ki fito mutanne gari su san ki ba. Maza sun mamaye lamarin, a koyaushe sai dai su nada mu mukamai. Idan ka nada mutum ba ya da bakin magana dole ne ya yi biyayya ga wanda ya nada shi. Kina ji kina gani za a yi ba daidai ba amma sai dai ki tsuke baki ki yi shiru.
Wadansu na ganin mata suna da rauni, ba ki ganin wannan a matsayin dalilinsu na ajiye matan a gefe?
Wannan ba dalili ba ne. Mun san cewa akwai raunin amma ba wanda zai hana ta shugabanci ba. Ai mukaman iri-iri ne idan ba za a ba mace mukamin shugabanci ba, to ai akwai wakilci. Me ya sa ba za a ba ta wakilci ba? Ko a gida mace ce wakiliyar maigida a yayin da ba ya nan. Amma wai sai namji ya rufe ido ya ce wai mace ba za ta iya ba, ya mance mace ce ta haife shi ta kuma raine shi.
Shin kina ganin idan an zabi matan za su iya sauke nauyin da aka dora musu?
kwarai kuwa. Mata fa su ne iyaye masu tausayin al’umma. Da suka san zafin haihuwa. Idan mace ta je bangaren lafiya na tabbata za ta yi iya kokarinta wajen ganin ta samar da asibitoci a cikin lungu da sako don taimaka wa mata wajen haihuwa da kuma kula da yara. Idan kika je Majalisar Jihar Kano za ki tarar duk maza ne ke shugabantar kwamitocin da ke kula da mata da kananan yara. Ta yaya kike zaton namiji zai iya kula da abin da bai san kansa ba? Shi ya sa muke ta fafutika mu ga mata sun samu mukamai saboda a duk inda ka samu wani abu da ya shafi mata to ya fi kyau mace ta gudanar da lamarin. Hausawa sun ce ciwon ’ya mace na ’ya mace ne. Mata suna da amana da tsentseni na rike kudi, ba za ka samu mata da cin hanci ba. Da a ce matan ne ke rike da mukamai to da an samu gyara a harkar tafiyar da kasar nan. Za a samu sauki a cikin tabargazar cin hanci da rashawa. Yanzu ki dauki irin yadda ake yi wa mata fyade a sansanin ’yan gudun hijira, da a ce mata ce ke rike da wuraren to wallahi da an samu gyara sosai, don ba za su yarda irin hakan ta ci gaba da faruwa ba.
A yanzu me kuke so shugabanni su yi muku?
Lokacin da a ka yi taron Ranar Mata na bara mun gaya wa dukan shugabannin jam’iyyun siyasar nan cewa idan har ana so a rika zaben mata a mukaman siyasa to dole sai an raba mukaman shugabancin jam’iyya da mata, ba wai kawai a ba su mukamin shugabar mata ba. Mace za ta iya yin Mataimakiyar Shugaban Jam’iyya ko Ma’aji ko Sakatariya da sauransu. Idan mata suna da wadannan mukamai ne suke da muryar da za su yi magana a saurare su. Idan aka samu mata suna rike da manyan mukaman za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an tsayar da mace a mukamai daban-daban har su kai ga nasarar cin zabe. Ya kamata kowace jam’iyya ta ware wasu kujeru ga mata. Duk da ba Jam’iyyar APC nake ba lokacin da Gwamnan Kano ya bayar da rikon kwarya ya bayar da kujerun kansiloli ga mata a dukan kananan hukumomi, muna ta murna a kan hakan, sai dai da aka zo zabe babu mace ko daya da ta samu takara ballantana a kai ga zabenta. Amma idan ana so mu wakilci jama’armu to a ba mu dama mu fito mu tsaya takara a zabe mu. Kada a manta fa mu da ’ya’yanmu ne ke fitowa zabe. Mu jure wa rana da sanyi amma mu an ki a ba mu dama wannan ba daidai ba ne.
Ya kamata Hukumar Zabe ta tilasta wa jam’iyyu su fito da wani tsari da za a bayar da gurbi ga mata, duk kuma jam’iyyar da ba ta bi wanann tsari ba, ma’ana ta kawo sunayen ’yan takarar babu mata a ciki a mayar mata a nuna mata sai ta gyara wannan kuskuren kafin a karba.
Sannan jam’iyya ta rike girmanta ta daina zama ’yar amshin shatan masu mulki. Jam’iyya tana da karfin hukunta duk wani danta koda kuwa Shugaban kasa ne, domin ita ya taka ya hau wannan kujera. Don haka jam’iyya tana da karfi.
Wane kira kike da shi ga mata, musamman ’yan siyasa?
Ina kira ga mata musamman ’yan siyasa da kada mu gajiya, mu daure mu ci gaba da yin abin da muke yi. Wata rana za a kai ga nasara ko ba a kanmu ba, ’ya’yanmu za su samu. A yanzu akwai yara ’yan mata da muke koya musu siyasa, to muna sa rai za su samu nasara. Tun a taron Beijin aka fito da batun za a ba mata mukamai amma har yanzu wannan abu ba a kai ga samunsa ba. Su ma kungiyoyin mata da ke Gwamnatin Tarayya babu abin da suke yi mana a wannan bangare. Mata mu dage mu nemi ilimi da neman na kai. Idan ya zama muna da ilimi muna kuma da abin hannunmu to muna zaune za a zo a nemo mu a siyasar, dama ita ce bangaren da aka yi mana zarra.