An kaddamar da gidan rediyon Dandal Kura

A makon jiya ne Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya jagoranci bude gidan Rediyon Dandal Kura mai watsa shirye-shirye da harsunan Hausa da Barbanci a wani biki da aka gudanar a garin Maiduguri.Manajan Daraktan Rediyon Dandal Kura, Alhaji Faruk dalhatu, ya bayyana wa wakilinmu jim kadan da kaddamar da gidan rediyon, cewa ya bude […]

An kaddamar da gidan rediyon Dandal Kura
An kaddamar da gidan rediyon Dandal Kura

A makon jiya ne Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya jagoranci bude gidan Rediyon Dandal Kura mai watsa shirye-shirye da harsunan Hausa da Barbanci a wani biki da aka gudanar a garin Maiduguri.
Manajan Daraktan Rediyon Dandal Kura, Alhaji Faruk dalhatu, ya bayyana wa wakilinmu jim kadan da kaddamar da gidan rediyon, cewa ya bude tashar rediyon ne domin farfado da dabi’u da al’adun Barebari  da suke zaune a yankin Tafkin Chadi da ya hade kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi kuma suke da dimbin tarihi da jama’a sama da miliyan 10.
Faruk dalhatu ya ce dalili na biyu shi ne yankin ya kwashe shekara bakwai yana fama da bala’in yakin Boko Haram, al’amarin da ya kusan ruguje yankin, sannan ga galibin kafofin watsa labarai, suna karin gishiri kan labaran da suke bayarwa game da halin da ake ciki yankin.
Ya ce babban burinsu su karfafa wa mutanen gwiwa su gyara yankin a kokarin da suke yi kan yadda za a sake farfado da yankin Arewa maso Gabas da ke baya ga dangi tun kafin aukuwar wannan matsala sakamakon yadda talauci ya yi katutu a tsakanin al’ummar yankin ga rashin aikinyi a tsakanin matasa, inda suke fatar zaburar da su wajen neman ilimi da dogaro da kai. “Wadannan  su ne manyan dalilan da suka zaburar da ni na yi sha’awar bude wannan gidan rediyo don jama’ar yankin su tafi da zamani a kuma samu ci gaban da ya dace. A gaskiya akwai gibin wajen samun bayanai da labarai na hakikanin abin da ke faruwa a yankin wanda in ka shigo za ka ga abin da kake ji ba haka ba ne, wato labaran da ake bayarwa daban ne da abin da yake faruwa,” inji shi.
Faruk dalhat, ya ce gidan rediyon ya dada fito da harshen Barbanci a duniya inda ya ce ci gaba ne da suke hada Barbanci da Hausa, “Ina so in fada maka a duk duniya mu ne muka fara watsa shirye-shirye da harshen Kanuri kuma ana sauraronmu a kasashen duniya daba-daban, irin su kasashen Rasha da Saudiyya da Bangladash da Gabas ta Tsakiya da Pakistan da Sudan da Afirka ta Tsakiya da sauransu inda muke samun sakonnin gaisuwa da yabo da shawarwari da ra’ayoyi,” inji shi.
 Sai ya roki al’ummar yankin su ci gaba da addu’ar Allah Ya kawo karshen wannan yakin da ake yi da Boko Haram, kuma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken hadin kai da goyon baya ta yadda za a kawo karshen yakin.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland