An kaddamar da gidauniyar Ala

A ranar Lahadi 1 ga watan Satumba, 2013 ne fitaccen mawakin Hausa Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da (Ala) ya shirya wani gagarumin taro na karrama mutanen da suka ba shi gudunmuwa a harkarsa ta waka, tare da kafa wata gidauniya a karkashin kamfaninsa da za ta rika taimaka wa marasa galihu.Taron, wanda […]

An kaddamar da gidauniyar Ala

Hoton bayan taro Daga hagu Mawaki Rabi’u Dalle da Ado Ahmad Gidan Dabino da Hakimin Dala, Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma mawaki Misbahu Ahmad a lokacin kaddamar da gidauniyar AlaA ranar Lahadi 1 ga watan Satumba, 2013 ne fitaccen mawakin Hausa Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da (Ala) ya shirya wani gagarumin taro na karrama mutanen da suka ba shi gudunmuwa a harkarsa ta waka, tare da kafa wata gidauniya a karkashin kamfaninsa da za ta rika taimaka wa marasa galihu.
Taron, wanda aka gudanar a dakin karatu na Murtala Muhammad da ke Kano, ya samu halartar sarakuna da malaman addini da kuma manyan malaman jami’o’in Arewa.
Da yake jawabi a matsayinsa na uban taro, Hakimin Dala Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna farin cikinsa ga yadda Ala ya shirya irin wannan taro, musamman ma tunaninsa na kafa gidauniya domin tallafa wa al’umma inda ya ce “Hakan ya nuna gudunmuwarsa ba ga waka kadai ta tsaya ba har ma da taimakawa al’umma da karfinsa.”
Hakimin Dala ya yi kira ga mawaka da su rika sanya tarbiyya ta addini a cikin wakokinsu kamar yadda Ala yake yi, domin a cewarsa duk abin da Musulmi zai yi a rayuwa dole ne ya zama addini shi ne a gaba.
Shi ma da yake nasa jawabin, babban bako mai jawani, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, wanda Farfesa Abdulkadir dangambo ya wakilta ya bayyana irin halin da wakokin Hausa suka samu kansu tun bayan  rugujewar Daular Usmaniyya inda yake cewa, “Tun bayan wakoki irin na su Shehu Mujaddadi sai ya zamo harkar waka ta shiga wani hali na rashin tsafta da tarbiyya. Hakan ya zama sai daidaikun mawaka ake samu suke tafiyar da wakarsu cikin tsari. To shi Aminu yana cikin kadan daga cikin mawakan da wakokinsu suke kamanta bin tsari, domin kuwa awai sako na ilimantarwa a cikin wakokin nasa.” Inji shi.
Manyan masana da dama dai sun yi jawabai a wajen inda daga baya kuma aka kaddamar da Gidauniyar wacce Alhaji Sani Lawan kofar Mata ya kaddamar da ita da kudi N250,000. Daga bisani kuma mutane suka yi ta ba da tasu gudunmuwar don tallafawa gidauniyar.
Da yake jawabi game da manufar kafa wannan gidauniya Mawaki Aminu Ala ya bayyana cewa tun farko masoyansa ne wadanda suka kafa dandalin Ala a kafar sadarwa ta facebook suka nemi da ya kafa wannan gidauniya. “Masoya wadanda suka kafa dandalin Ala a facebook suka bijiro da wannan tunani, wanda bayan na yi nazari a kai na ga cewar akwai alfanu a cikin yin hakan, ga shi kuma yau Alhamdu lillahi Allah Ya nufa an kaddamar da ita. Har ila yau wannan gidauniya za ta kula da abubuwa masu yawa musamman ta fuskar ci gaban harkar wakokin Hausa da kuma tallafa wa marayu a cikin al’umma. Idan misali an sami wani mawaki ya yi waka kuma ba shi da karfin buga wakar, to wannan gidauniya za ta dauki nauyin buga masa wakar da sauran ayyuka masu yawa” Inji Alan waka.  
A karshen taron an karrama mutane da dama wadanda suka ba Aminu gudunmuwa ta bangaren waka. Kadan daga cikinsu su ne Sani Lawan kofar Mata, Farfesa Sa’idu Muhammadu Gusau da Hakimin Dala Alhaji Aminu Ado da Malam Ibrahim Sheme da kuma Hajiya Gaji Fatima dantata da sauransu.