An kaddamar da Gidauniyar Zama Lafiya ta Sarkin Sasa
A ranar Lahadin makon jiya aka kaddamar da gidauniyar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, a Ibadan, wadda za a kashe Naira miliyan 50 domin gina cibiyar da ta kunshi zauren taro da dakin karatu da dakunan wasanni, wadda aka yi wa lakabi da Cibiyar Zama Lafiya ta Sarkin Sasa, don hadin kan matasa da ci […]
A ranar Lahadin makon jiya aka kaddamar da gidauniyar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, a Ibadan, wadda za a kashe Naira miliyan 50 domin gina cibiyar da ta kunshi zauren taro da dakin karatu da dakunan wasanni, wadda aka yi wa lakabi da Cibiyar Zama Lafiya ta Sarkin Sasa, don hadin kan matasa da ci gabansu a sashen Kudu maso Yammacin kasa.
Wani mai sha’awar harkokin wasanni a Ibadan, mai suna Cif Dapo Josua shi ne ya jagoranci kaddamar da asusun a filin wasanni na Lekan Salami da ke Adamasingba a Ibadan.
Cif Dapo Josua ya ce, sun yanke shawarar sanya sunan Sarkin Sasa ne, a matsayin sunan gidauniyar saboda irin fafutukar da ya yi cikin shekaru 31 a kan karaga yana jagorancin al’umma, domin hada kawunansu da samar da zama lafiya a tsakanin kabilu kasa ba tare da nuna bambanci ba.
Gimbiya Adebisi Adegoke ce ta wakilci Uwargidan Gwamnan Jihar Oyo, Madam Florence Ajimobi a wajen bikin. Kwamishinonin matasa da wasanni na jihohin Osun da Ogun sun aika da wakilai zuwa wajen wannan biki, wanda shi ne irinsa na farko da wani dan Arewacin kasa ya samu shiga cikin jerin sunayen manyan mutane da za a rika tunawa da su ta fannin gudunmawar da suka bayar ga hada kawunan matasa da ci gabansu. Sarakunan Hausawa daga jihohi shida na Yammacin kasa, tare da dimbin jama’arsu ne suka rufa wa Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, baya zuwa wajen wannan biki.
Shugabannin al’umma da suka aike da wakilai sun hada da Aare musulmi na kasar Yarbawa Alhaji Abdul Azeez Arisekola Alao da Babban Lauya Cif Afe Babalola da Eze Ndigbo Dakta Aled Anozie.
An shirya wasan kwallon kafa a tsakanin kulob biyu na matasa masu suna Eagale Babe da Abbey Lincom, wadanda suka shafe mintuna 90 suna fafatawa, domin lashe kofin Sarkin Sasa a tsakaninsu. An kawo karshen wasan kowane kulob yana da kwallo daya. Alkalan wasan sun yanke shawarar yin bugun fanariti bayan karin wa’adi, wanda aka yi canjaras. Kulob din Abbey Lincom shi ne ya yi nasara da ci biyar a yayin da Eagle Babe ta ci kwallaye 4. Shugaban majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na kudancin kasa, Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, shi ne ya mika wa kyaftin din Abbey Lincom babban kofin.
An karshen wannan biki an karrama wasu mutane da lambar yabo, wadanda suka hada da Sarkin Samarin jihohin yamma, Alhaji Nasiru Yaro da Sarkin Fulanin Randa, Abeokuta, Alhaji Muhammed Kabiru da Sarkin Nufawan Ibadan, AlhajiShehu Ibrahim.