An kaddamar da Inshorar Takaful a Kano

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya shawarci hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma  su rungumi shirin nan na inshorar Musulunci, wato Takaful Insurance, Sarkin ya yi wannan roko ne a ranar Litinin da ta gabata a lokacin bikin kaddamar da Kamfanin Takafaul reshen Jihar Kano da Bankn Kasuwanci […]

An kaddamar da Inshorar Takaful a Kano

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya shawarci hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma  su rungumi shirin nan na inshorar Musulunci, wato Takaful Insurance, Sarkin ya yi wannan roko ne a ranar Litinin da ta gabata a lokacin bikin kaddamar da Kamfanin Takafaul reshen Jihar Kano da Bankn Kasuwanci na Ja’iz ya samar da shi, wanda kuma aka gudanar da shi a fadar Sarkin da ke kofar Kudu cikin birnin Kano. 

Malam Muhamamdu Sanusi II ya ce idan har aka gudanar da tsarain kamar yadda addinin Musulunci ya tsara za a rage matsalolin tatatlin arziki a tsakanin al’umma ta hanyar taimakekeniya. “Kama yadda aka sani lokacin da muna aiki a Babban Bankin kasa (CBN( mun tsaya akan lallai mu ga yadda Najeriya za ta zama cibiya ta harkokin tattalin arziki da aka gina su akan shari’a. Wannan abu ne da ya dace, muna fatan za a sami karin bankuna da karin kamfaninnika na takaful, sabida samun bunkasar tattalin arziki”

A jawabinsa Shugaban Gudanarwar Daraktocin Bankin Jaiz Alhaji Umar Mutallib ya  bayyana cewa an samar da inshorar takaful ne a bisa doron tsarin addinin Musulunci da nufin tallafa wa gwamnatoci da kananan ‘yan kasuwa wajen magance matsalolin tattalin arziki da suke fuskanta. 

“Alhamdulillahi mun nemi izini na gwamnati mun samu lasin na tafiyar da kamfanin isnhora na Musulunci.  Inshora ce ta Musulunci wanda duk wani abu da ba ya cikin haddi ba za a iya tafiyar da shi ba” 

Shi kuwa Shugaban Sashen Tallace-tallace na kamfanin inshorar takaful din Alhaji Aliyu Buhari ya shawarci al’’umma da su yi kokarin rajista ga kamfanin na Ja’iz Takaful duba da cewa shi ne tsarin inshora da ya yi daidai da tsarin addinin Musulunci domin tsare dukiyar da Allah ya ba su. 

Ya bayyana cewa tsarin inshorar iri biyu ne, wanda ya shafi inshorar iyali da ta dukiya wanda kuma babu kudin ruwa a ciki sai dai kamfanin ya juya  maka kudinka wanda tuni bankin ya hada kai da wasu manyan kamfanoni a fadin duniya “Musulunci ya yarda akan duk wata tafiya da za a yi indai akan alheri ne, matukar bai saba wa ka’idar shari’a ba. 

Takaful yana tafiya kan ka’idoji guda biyu na farko akwai Ta’awun wanda shi ne gamayya ta hada kai domin taimakekeniya na biyu kuma akwai tabarru wato gudummmawa”. 

Ita ma a nata jawabin Babbar Akantar Jihar Kano Hajiya Aishatu Muhammad Bello ta jaddada kudurin gwamnatin Kano na shiga a dama da ita cikin wanann tsari na takaful “Inshorar takaful ta samu ne saboda goyon baya da Mai martaba Sarkin Kano ya ba wa fannin tsare-tsare da suke da muhimmanci  ga rayuwar al’ummar kasar nan a lokacin da yake Gwamnan Babban Bankin kasa.”

 

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50