An kaddamar da Kotun Ta fi-da-gidanka kan tsabtace muhalli a Nasarawa
Babban Jojin Jihar Nasarawa Mai shari’a Suleiman Umaru Dikko ya kaddamar da Kotun Tafi-da-Gidanka kan tsabtace muhalli a Jihar Nasarawa. A jawabinsa Mai shari’a Suleiman Dikko ya ce kafa kotun na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na samar da ingantaccen muhalli a jihr, kuma an raba kotun zuwa shiyoyi uku da ke jihar inda za […]
Babban Jojin Jihar Nasarawa Mai shari’a Suleiman Umaru Dikko ya kaddamar da Kotun Tafi-da-Gidanka kan tsabtace muhalli a Jihar Nasarawa.
A jawabinsa Mai shari’a Suleiman Dikko ya ce kafa kotun na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na samar da ingantaccen muhalli a jihr, kuma an raba kotun zuwa shiyoyi uku da ke jihar inda za ta gudanar da ayyukanta ne da dokar tsabtace muhalli ta jihar da ta maye gurbin tsohuwar dokar tsabtace muhalli ta 1997. Sai ya yi kira ga alkalan kotun su tabbatar sun gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko son zuciya ba.
A jawabin Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar, Misis Abigail Waya ta koka ne kan yadda jama’a ke zubar da shara ba bisa ka’ida ba a jihar, inda ta bayyana cewa wadnnan kotuna da aka kaddamar za su taimaka wajen tsabtace muhalli a jihar.
Ta shawarci al’ummar jihar baki daya su tabbatar sun bi dokokin tsabtar muhalli don kare mutuncinsu.
Mataimakin Janar Manaja mai kula da harkokin shari’a na Hukumar Bunkasa Birane ta Jihar, Barista Usman Lamus ya ce an dade ana bukatar irin wadannan kotuna da ya ce za su taimaka wajen tabbatar da ana bin dokar tsabtace muhalli a jihar.
Da yake jawabi a madadin alkalan kotunan, Mista Habila Abindaga ya ce za su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana, inda ya bukaci a ba su cikakken goyon baya domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Wadanda aka nada a matsayin alkalan kotunan sun hada da Mai shari’a Abdullahi Shama Umar wanda zai kula da Shiyyar Kudancin Jihar, sai Ibrahim Shekarau Muhammed da zai kula da na Shiyyar Arewa, sai Habila Abindaga wanda zai kula da Shiyyar Yamma.