An kaddamar da kungiyar mata masu Keke-Napep ta Jihar Filato

A ranar Asabar aka gudanar da taron kaddamar da kungiyar mata masu Keke Napep ta Jihar Filato a garin Jos.Yayin bikin an kuma bude ofishin kungiyar.Da yake jawabi a wajen taron Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato Alhaji Abubakar Abdullahi Dashe ya bayyana matukar farin cikinsa sakamakon kafa kungiyar mata masu Keke-Napep. Ya yaba wa matan […]

An kaddamar da kungiyar mata masu Keke-Napep ta Jihar Filato
An kaddamar da kungiyar mata masu Keke-Napep ta Jihar Filato

A ranar Asabar aka gudanar da taron kaddamar da kungiyar mata masu Keke Napep ta Jihar Filato a garin Jos.
Yayin bikin an kuma bude ofishin kungiyar.
Da yake jawabi a wajen taron Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato Alhaji Abubakar Abdullahi Dashe ya bayyana matukar farin cikinsa sakamakon kafa kungiyar mata masu Keke-Napep.
Ya yaba wa matan da suka kafa kungiyar sakamakon kokarin da suka yi wajen ganin ba a bar mata a baya ba.
Ya ce “Ina yaba wa matan kungiyar musamman shugabar kungiyar bisa kokarin da suka wajen kafa kungiyar, wanda haka yake nuna mata ba sa so a bar su a baya.”
Ya ce babu shakka wannan kungiya tana taimaka wa gwamnatin jihar musamman wajen bunkasa harkokin sufuri a jihar.
Ya ce, a shirye gwamnatin jihar take wajen ganin ta yi aiki da wannan kungiya don a bunkasa harkar sufuri a jihar.
A nasa jawabin shugaban kungiyar masu tuka Keke Napep na Jihar Filato (TRUN) Elder Yakubu Jatau ya ce kungiyar za ta taimaka wajen magance matsalolin a harkar sufuri a Jihar Filato.
Ya ce “Babu shakka wannan kungiya za ta taimaka wa wannan harka ta Keke Napep a Jihar Filato, sannan wacce aka zaba a matsayin shugabar  kungiya mace ce mai kokari wadda ta taimaka wajen ba wa matasa kekunan Napep a garin Jos. Don haka muna goyon bayan wannan kungiya kuma muna goyan bayan wannan mata.”
Tun da farko a nata jawabin shugabar kungiyar  Hajiya Umma Hassan ta  ce sun kafa wannan kungiya don su taimaka wa junansu a kan wannan harka ta Keke Napep.
Ta ce akwai wasu matan da suke sayen Keke Napep, amma ba su san yadda za su bayar da su ba.
“Mambobin kungiyarmu akalla za mu kai 150, kuma a cikinsu akwai mace daya da take da Keke Napep sama da 100, inda ta raba wa matasa a garin Jos.”
Ta ce babu shakka akwai ci gaba a wannan sana’a domin sun samar wa matasa da dama ayyukan yi.
Ta shawarci wadanda suka ba matasa Keke Napep, su yi kokari, don yin dukkan abubuwan da suka kamata kafin su ba su kekunan Napep din.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya