An kaddamar da kungiyar Matasan Fulani a Minna

A kwanakin baya ne Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal-Hore na kasa Alhaji Bello Abdullahi Badejo ya kaddamar da Shugaban kungiyar Matasa Alhaji Bello Ahmad Garatu a garin Minna, a matsayin daya daga cikin yunkurin da Majalisar kungiyar ke yi na ba ilahirin ‘ya’yanta don cimma burin da aka sa a gaba na habbaka harshen Fillanci […]

An kaddamar da kungiyar Matasan Fulani a Minna
An kaddamar da kungiyar Matasan Fulani a Minna

A kwanakin baya ne Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal-Hore na kasa Alhaji Bello Abdullahi Badejo ya kaddamar da Shugaban kungiyar Matasa Alhaji Bello Ahmad Garatu a garin Minna, a matsayin daya daga cikin yunkurin da Majalisar kungiyar ke yi na ba ilahirin ‘ya’yanta don cimma burin da aka sa a gaba na habbaka harshen Fillanci da kuma al’adunsu wadanda ba su saba ma addinin Musulunci ba.

Alhaji Bello Abdullahi Badejo wanda ya samu rakiyar tawagarsa da ta hada da Shugabannin rassan kungiyar da ke jihohi daban-daban,ya ja hankalin matasan da aka kaddamar da su san da cewa su ne kashin bayan ciyar da kowace al’umma gaba,don haka ya kamata su fito da shirye-shiryen da suka kamata wadanda za su taimakawa kungiyar domin samun nasarorin da suka sa a gaba na yaki da jahilci,da kuma zaman kashe wandon da ya zama ruwan dare a tsakanin matasa musamman a wannan zamanin.
Shugaban kungiyar wanda ya yi amfani da wannan damar wurin kira ga al’ummar Fulani baki daya da su ba sabbin Shugabannin da aka zaba a dukkan matakai cikakken hadin kai da goyon baya.Yin haka,zai ba su damar bayar da gudunmuwar da ya kamata domin shawo kan muhimman matsalolin da suka addabi rukunin wadannan mutanen na satar dabbobin da ta dade suna ci musu tuwo a kwarya,bayan matsalar fama da karancin makiyaya a sassa daban-daban da ke kasar nan.
Dangane da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Shugaban kungiyar ya yi imanin zai ba mara da kunya. Ya ce musamman idan aka yi la’akari da halin da kasar nan ta samu kanta a ciki,musamman tun da aka sake daura ta a turbar mulkin dimukradiyya a shekarar 1999. Ya ci gaba da cewa: “Bisa la’akari da haka ne za mu dauki wadannan matakan, na farko za mu taimaka masa da addu’o’i fiye da yadda ake tsammani, sannan muna bukatar a samar mana da matsugunin da za mu zauna na dindindin. Mun ga illolin tafiye-tafiye da sunan tashi. Yin haka, ya sa da dama daga cikin mutanenmu sun yi asarar dukiyoyinsu,wasu ma har da rayukansu,” inji shi.
Shugaban kungiyar Shiyyar Arewa Ta Tsakiya, Alhaji Sani Juli,ya jaddada wa Shugaban Matasan da a shirye suke su bashi cikakken hadin kan da za su aiwatar da wannan gagarumin aikin da ke gabansu na bayar da gudunmuwa a fannoni daban-daban da Fulani ke fuskantar matsalolin a ciki wadanda suka hada da kiwo,da neman ilimin boko,da na addini,da kuma fannin kiwon lafiya.