An kaddamar da kungiyar tsaro a Adamawa don magance rikicin manoma da makiyaya
An kaddamar da wata kungiyar tsaro mai suna CUSAL a Jahar Adamawa domin taimaka wa jami’an tsaro su gudanar da aikinsu yadda yakamata a fadi Jahar Adamawa. An kaddamar da kungiyar ne a harabar makarantar sakandare na jeka ka dawo na gwamnati da ke Unguwan Luggere a cikin garin Jimeta da ke karamar hukumar Yola […]
An kaddamar da wata kungiyar tsaro mai suna CUSAL a Jahar Adamawa domin taimaka wa jami’an tsaro su gudanar da aikinsu yadda yakamata a fadi Jahar Adamawa.
An kaddamar da kungiyar ne a harabar makarantar sakandare na jeka ka dawo na gwamnati da ke Unguwan Luggere a cikin garin Jimeta da ke karamar hukumar Yola ta Arewa.
Shugaban kungiyar Sheikh Sa’ad Jimeta, ya nuna farin cikinsa da ba shi shugabancin wannan kungiya, sannan ya yi alkawarin hada kai da jami’an tsaro wajen kai musu ruhotannin wadanda ake zargin za su iya yin ta’addanci ko kawo tashin hankali a tsakanin al’umma.
Ya shawarci mambobinsa da su kasance masu yin taka-tsan-tsan a duk lokacin da suke gudanar da aikinsu domin gudun shiga hurumin da ba nasu ba.
Ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar da su kasance yi wa shugabansu biyayya da bin doka yadda ya dace, domin daga martabar kungiyar da kuma samun nasara a duk abin da suka sanya a gaba.
Sheikh Sa’ad ya kuma bukaci al’umma su ba su hadin kai da goyon baya domin cim ma burinsu wajen kawo karshen matsalar tsaro a Jahar Adamawa.