An kaddamar da littafin addu’o’i a Musulunci
kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah reshen Jihar Legas ta kaddarmar da sabon littafi kan yadda ake yin addu’a bisa tsarin addinin Musulunci.An gudanar da taron kaddamar da littafin ne mai suna ‘Tace addu’a a cikin Ibada’ wanda aka wallafa cikin harshen Larabci a unguwar Festac a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.Mawallafin […]
kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah reshen Jihar Legas ta kaddarmar da sabon littafi kan yadda ake yin addu’a bisa tsarin addinin Musulunci.
An gudanar da taron kaddamar da littafin ne mai suna ‘Tace addu’a a cikin Ibada’ wanda aka wallafa cikin harshen Larabci a unguwar Festac a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.
Mawallafin littafin Malam Ahmed Sale, ya ce ya wallafa littafin ne saboda ya fadakar da mutane kan yadda ake yin addu’a da kuma muhimmancinta.
‘Na wallafa wannan littafin ne saboda nanuwa jama’a yadda ake yin addu’a da matakan da ake bi wurin yin addu’a. Kamar yadda manzon Allah ya yi mana bayanin cewa wani bawan Allah matafiyi wanda ba a karbi addu’arsa ba duk da cewa matafiyi ne saboda haramun da yake yin ta’ammuli da ita. To idan wannan bawan Allah ya roki Allah da sunansa na Rabbi, amma ba a amsa masa addu’arsa ba, to akwai dalili. Mu ma a yanzu idan muka yi addu’a ba a amsa mana ba to akwai dalili. Shi ya sa na wallafa wannan littafi don fadakar da jama’a’.
Malam Ahmad wanda har ila yau shi ne limamin masallacin Juma’a na layin ’yan kaji da ke kasuwar Alaba Rago, ya bayyana cewa rashin kudi shi ne babban kalubalen da ya fuskanta yayin da yake rubuta littafin.
‘Ka ga saboda rashin kudi kwafi dubu daya kawai na wallafa da aka je wurin kaddamar da shi sai littafin ya yi karanci, domin kafin wani lokaci an saye duka kofin da muka kai wurin. Ka ga da a ce akwai isassun kudi da mun buga fiye da dubu daya’ Inji shi.
Ya bayyana cewa ya wallafa litttafai da dama a fannoni daban-daban domin fadakar da jama’a.
Ya dage a kan cewa ya zabi harshen Larabci saboda shi ne yaren addinin Musulunci na duniya gaba daya.
Ya bayyana cewa wasu bayin Allah sun yi alkawarin daukar dawainiyar buga littafin ta hanyar fassara shi zuwa harshen Hausa da kuma Turanci.