An kaddamar da littafin aikin hajji a Gombe

A ranar Litinin din da ta gabata ne aka kaddamar da littattafai guda uku wanda Salihu Abdullahi Jarman Kumo, ya rubuta akan aikin Hajji don amfanin mahajjata a kasa mai tsarki.A jawabinsa a wajen taron gwamna jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, umurni ya bai wa hukumar jin dadin alhazai ta jiha da taje tayi […]

An kaddamar da littafin aikin hajji a Gombe

Bangon Littafin Aikin HajiA ranar Litinin din da ta gabata ne aka kaddamar da littattafai guda uku wanda Salihu Abdullahi Jarman Kumo, ya rubuta akan aikin Hajji don amfanin mahajjata a kasa mai tsarki.
A jawabinsa a wajen taron gwamna jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, umurni ya bai wa hukumar jin dadin alhazai ta jiha da taje tayi nazarin yawan kwafin da suke da bukata a saya don rabawa
mahajjata na wannan shekarar da  shekaru uku nan gaba. Gwamna dankwambo, wanda mai bashi shawara kan aikin hajji Alhaji Sa’adu Hassan, ya wakilta yabawa marubucin littafin ya yi bisa yadda ya jajirce wajen rubuta wannan littafi har ya fito.
A  jawabinsa wajen taron Khadi Ibrahim Babbawa, wanda shi ne shugaban hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Adamawa kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta kasa reshen jihar Adamawan ya yaba wa marubucin littafin tare da cewar ya kamata a ba shi goyon bayan da ya kamata saboda ya yi kokari matuka.
Khadi Ibrahim Babbawa, ya bayyana aikin hajji da cewa aiki ne da ake kashe kudi masu yawa don haka yana da kyau mutum ya fahimci yadda ake gudunar da aikin kafin ya isa kasar.
A cewar sa saboda ingancin littafin zai yi magana da Gwamnatin Adamawa da kuma hukumar jin dadin alhazai ta jihar don sayen kwafi masu yawa da za a raba wa mahajjata a wannan shekarar dama shekaru masu zuwa na gaba, don su fahimci yadda ake aikin.
Shi kuwa babban bako mai jawabi a wajen taron, Alhaji Umar Kwairanga Sarkin Fulanin Gombe, wanda ya samu wakilcin Shugaban kungiyar Lauyoyi musulmi ta kasa Barista Abdulganiy Bello, cewa ya yi littafin ya fito a lokacin da ya dace tunda yanzu ne ake kokarin tafiya aikin hajjin kuma a Gombe mafi yawan mahajjatan sababbi ne.
Alhaji Umar Kwairanga, ya kara da cewa wannan littafi alheri ne ga mahajjata kuma ga shi an rubuta shi da Hausar Boko wadda kowa zai iya karantawa ya gane kafin lokacin tafiya aikin hajjin.
Daga nan sai yayi godiya ga mawallafin Salihu Abdullahi, tare da yi masa addu’ar alheri game da cewa suna jiran ranar da zai fitar da littafin da ya rubuta na tarihin Firayiministan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.
Babban mai kaddamar da littafin Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, nuna farin cikin sa ya yi kan yadda aka rubuta littafin, akan aikin hajji wanda ya nuna cewa marubucin cikakken mai kishin addini ne, inda ya ce
da wani mai neman kudi ne da zai rubuta ne akan tarihin wani dan siyasa ko gwamnan jihar don ya samu  kudi.
Ya sayi kwafin uku na littatafan akan kudi Naira miliyan uku, tare da yin kira ga sauran jama’a da cewar su saya don taimaka wa addini.
Shugaban hukumar alhazai ta kasa Alhaji Muhammad Musa Bello, ya jinjina wa marubucin littafin bisa yadda ya rubuta shi da harshen da mafi yawan jama’a za su fahimta.
Alhaji Muhammad Musa Bello, wanda ya samu wakilcin Alhaji Sale Okenwa daraktan tsare-tsare na hukumar ya ce duk mahajjacin da ya karanta wannan littafi ya rage musu aiki ne, sannan sai ya ce hukumarsu za ta sayi littattafan masu yawa don ajiyewa a dakin ajiyar takardu don a rika amfani dasu a lokutan bitar aikin hajji ga mahajjata.
Marubucin littafin Alhaji Salihu Abdullahi Jarman Kumo, cewa ya yi ba ya rubuta wannan littafi ne don neman kudi ba, ya rubuta ne don taimakon addinin Musulunci da Musulmi a lokacin da suke aikin hajji a kasa mai tsarki
Littattafan guda uku masu suna Aikin Hajji a Aikace da Aikin Hajji a hukunce da Addu’o’i a kasa mai tsarki suna da shafuka 76 ne da 68 da kuma 44.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano