An kaddamar da na’urar da za ta magance satar shanu
Shugabannin Fulani makiyaya na jihohin Kudu Maso Yamma sun yi taron haɗin gwiwa da jami’an kamfanin MTN, wanda ya ɓullo da na’urar lambar saniya domin magance matsalar nan ta satar shanu wacce ta daɗe tana addabar al’umar Fulani a Najeriya. Taron ya gudana a ƙarƙashin jagorancin sarkin Fulanin Jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambaɗo a fadarsa […]
Shugabannin Fulani makiyaya na jihohin Kudu Maso Yamma sun yi taron haɗin gwiwa da jami’an kamfanin MTN, wanda ya ɓullo da na’urar lambar saniya domin magance matsalar nan ta satar shanu wacce ta daɗe tana addabar al’umar Fulani a Najeriya.
Taron ya gudana a ƙarƙashin jagorancin sarkin Fulanin Jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambaɗo a fadarsa a ƙarshen makon jiya.
A jawabinsa, babban manajan kamfanin MTN a Najeriya, Aliyu Muhammad ya shaida cewa la’akari da muhinmmancin sana’ar kiwo ga al’ummar Fulani da ma tattalin arzikin ƙasa, kamfanin MTN ya yi haɗin gwiwa da takwaransa ‘Sponge Analitik’ inda suka samar da na’urar lambar shanu, wadda za a yi amfani da ita don magance matsalar satar shanu a ƙasar nan.
Babban jami’in masana’antar fasahar da ta yi haɗin gwiwa da MTN wajen samar da na’urar lambar, Ibrahim Maigari Ahmad wanda ya yi wa shugabannin Fulanin bayanin yadda na’urar take aiki a jikin saniya, ya shaida cewa za a yi wa dabbar allura ne a jikin fatarta, inda za a lika mata wata na’ura da girmanta bai kai kwayar shinkafa ba, sannan ba za a iya ganinta da ido ba sai da wata na’ura mai aiki da batir. Ya ce wannan na’ura za ta yi aiki ne tamkar wayar salula. “Idan an kai saniya kasuwa domin a sayar, jami’an kasuwar ne za su sanya na’ura su haska inda za su ga lambar a jikin saniyar, sai su tura wa wata lamba da MTN ta tanada, inda nan take za a turo masu da lambar mai saniyar da sunansa da kuma bayanan cewa shi ne ya ce a kai saniyar kasuwa ko kuwa sato ta aka yi. Sannan za a iya tura saƙon da kowane irin layi ba sai na MTN ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, baya ga rage matsalar satar shanu da fiye da kaso 60 bisa 100 da sabuwar hanyar fasahar za ta yi, za kuma ta bai wa ƙasar nan damar fita da shaununta ƙasashen Turai domin yin kasuwancinsu. “Alƙaluma sun nuna cewa Najeriya ce ke da kaso fiye da 45 na shanun da suke Yammacin Afirka, sai dai duk da haka ba ta fitar da shanunta ƙasashen Turai domin yin kasuwancinsu saboda ba ta amfani da tsari na lanbar saniya. Domin a ƙasashen da aka ci gaba, duk naman da za ka ci sai ka san daga inda yake. Wannan sabon tsari zai bai wa ƙasar nan damar fita da shanunta ƙasashen waje domin cinikinsu,” inji shi.
Hakazalika, Kwamishinan ayyuka na musamman a Jihar Osun, Oguntola Nudassiru wanda ya wakilci Gwamna Ra’uf Arebgesola a taron, ya yi lale marhabin da sabuwar fasahar lambar dabbobin. Ya ce tsari ne da zai magance salwantar dukiya da rayukan jama’a a Kudu maso yamma da ma Najeriya baki ɗaya.
Sarkin Fulanin Jihar Legas, Alhaji Muhammadu Bambaɗo ya jadadda aniyar Fulani na bai wa sabon tsarin goyon baya. Ya ce kaso 70 bisa 100 na shanun da ake yankawa a ƙasar nan, ana yanka su ne a jihohin Kudu maso yamma, sannan babu jihar da ake hada-hadar saniya tamkar Jihar Legas. “Haka ne ya sanya muka gayyato MTN domin su zo su kawo mana wannan fasaha a nan, domin idan aka magance matsalar shanun sata a wannan yanki, tamkar an yi maganin matsalar ne baki ɗayanta. Don haka za mu ba su goyon baya don magance matsalar da ta daɗe tana addabar al’ummarmu,” inji shi.
Mahalarta taron sun nemi rangwame a kan kuɗin lambar saniyar wanda yake Naira dubu 2 ga kowace dabba ɗaya, an kuma yi gwajin lambar a kan ɗaya daga cikin shanun sarkin na Fulanin Legas.