An kaddamar da ofishin kamfen na Buhari
Yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2019, Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu da abokin aikinsa na lafiya, Isaac Adewole da Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani da tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu da sauran membobin jam’iyyar APC jiya sun kaddamar da ofishin yakin neman zabe na shugaba Muhammadu Buhari a yankin kudu […]

Yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2019, Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu da abokin aikinsa na lafiya, Isaac Adewole da Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani da tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu da sauran membobin jam’iyyar APC jiya sun kaddamar da ofishin yakin neman zabe na shugaba Muhammadu Buhari a yankin kudu maso yammacin kasar.
Ofishin yakin neman zaben dai yana unguwar Mokola da ke cikin garin Ibadan a jihar Oyo.
Sai dai kuma Gwamna Abiola Ajimobi da sauran gwamnonin jihohin kudu maso yamma da shugabannin jam’iyyar na yankin da sauran manyan jam’iyyar na jihar ba su halarci taron ba.