An kaddamar da sababbin shugabannin Hukumar Alhazai ta Filato

Sakataren Gwamnatin Jihar Filato Farfesa Shedrack G. Best ya kaddamar da sabon shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Filato, Alhaji Ado Isma’ila Shigi da mambobin hukumar a sakatariyar gwamnatin jihar da ke Jos.Sauran mambobin hukumar da aka rantsar sun hada da Hajiya Sa’adatu Awatai da Alhaji Aminu Abubakar Atiku da Alhaji Shehu Gwandu da Alhaji Lawal […]

An kaddamar da sababbin shugabannin Hukumar Alhazai ta Filato
An kaddamar da sababbin shugabannin Hukumar Alhazai ta Filato

Sakataren Gwamnatin Jihar Filato Farfesa Shedrack G. Best ya kaddamar da sabon shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Filato, Alhaji Ado Isma’ila Shigi da mambobin hukumar a sakatariyar gwamnatin jihar da ke Jos.
Sauran mambobin hukumar da aka rantsar sun hada da Hajiya Sa’adatu Awatai da Alhaji Aminu Abubakar Atiku da Alhaji Shehu Gwandu da Alhaji Lawal Ango Gyang da Alhaji Muhammad Wahapna Usman da Alhaji Shu’aibu A. Dazimi da Alhaji danjuma Khalid da kuma Alhaji Hassan A. Sabo.
Da yake jawabi a lokacin a wurin kaddamarwar, Farfesa Shedrack Best ya yi kiran su gudanar da ayyukansu, kamar yadda tsarin hukumar ya tanada. “Wannan matsayi da aka nada ku wani matsayi ne mai matukar mahimmanci kuma gwamnatin Filato, ta nada ku ne saboda ganin cewa kun cancanta, bisa la’akari da irin matsayin da kuka rike a baya, don haka ku tsaya ku rike wannan amana ta hanyar gudanar da ayyukanku tsakani da Allah,” inji shi.
Da yake zantawa da wakilinmu bayan kaddamarwar, sabon shugaban hukumar, Alhaji Ado Shigi ya mika godiyarsu ga Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang, kan wannan dama da ya ba su.Ya ba da tabbacin cewa da yardar Allah a zamanin jagorancinsu, matsalolin da ake samu a hukumar a shekarun baya, za su zamo tarihi.
Ya roki maniyyatan jihar su bi dokokin kasa Mai tsarki, kuma su guji tafiya da kayayyakin da aka haramta tafiya da su.