An kaddamar da sabon sikelin awon nama da kifi a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da sabon sikelin awon nama da kifi ga ‘yan kasuwar Jihar. A lokacin da yake kaddamar da sabon sikelin a ranar Asabar din da ta gabata, Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatin ta bijiro da tunanin samar da sabon sikelin ne don ganin an sami […]

An kaddamar da sabon sikelin awon nama da kifi a Kano
An kaddamar da sabon sikelin awon nama da kifi a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da sabon sikelin awon nama da kifi ga ‘yan kasuwar Jihar.

A lokacin da yake kaddamar da sabon sikelin a ranar Asabar din da ta gabata, Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatin ta bijiro da tunanin samar da sabon sikelin ne don ganin an sami aminci a harkar saye da sayarwa, ta yadda zai zama babu cuta, babu cutarwa.
Ya ce sabon sikelin zai taimaka wajen samar da tsayayyen farashin nama da kifi ga masu amfani da su. Sannan ya gargadi ‘yan kasuwar da su yi amfani da sikelin awon kamar yadda addinin Musulunci ya tanada wajen ganin ba su tauye ma’auni ba. Shi ma a nasa jawabin Shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Kano Alhaji Abdullahi Sani Tofa ya bayyana cewa a matakin farko gwamnati ta samar da sikelin awon har guda 1600 don raba wa ga masu sana’ar kifi da nama a Jihar.
Ya kuma kara da cewa nan ba da dadewa ba Gwamnatin za ta samar da makamancin wanann sikeli ga masu sana’ar kayan ‘ya’yan itatuwa a jihar, don ganin su ma sun fara gudanar da cinikayyarsu a bisa tsarin auna hajarsu ga mai saye.
A wani ci gaban kuma gwamnatin jihar ta kaddamar da sabuwar kalandar Musulunci a jihar. Da yake bayani yayin kaddamar da kalandar gwamnan ya nemi jama’a da su rika amfani da lissafin watannin Musulunci a al’amuransu na yau da kullum. Da yake jaddada muhimmancin amfani da kalandar ta Musulunci, ya bayyana cewa a yanzu haka gwamnati ta bayar da kalandar domin raba wa ga makarantun jihar, a cewarsa hakan zai taimaka wa malamai da dalibai wajen yin amfani da kalandar a yayin koyo da kuma koyarwa.