An kaddamar da sabuwar makarantar Islamiyya ta al’umma a Bichi
An yi taron kaddamar da, tare da bude sabuwar makarantar “Madinatul Ahbab Wattalamiz Lawan Mai Kanti” mai zaman kanta kuma ta al’umma ta Islamiyya a garin Bichi na Jihar Kano. Taron, wanda ya samu halartar dimbin jama’ar garin Bichi da makwabta har da wasu daga birnin Kano, ya gudana ne a karkashin jagorancin shugaban majalisar […]

An yi taron kaddamar da, tare da bude sabuwar makarantar “Madinatul Ahbab Wattalamiz Lawan Mai Kanti” mai zaman kanta kuma ta al’umma ta Islamiyya a garin Bichi na Jihar Kano.
Taron, wanda ya samu halartar dimbin jama’ar garin Bichi da makwabta har da wasu daga birnin Kano, ya gudana ne a karkashin jagorancin shugaban majalisar limaman Juma’a na Jihar Kano, Sheikh Falalu dan-Almajiri, Fagge.
Makarantar, wadda wani babban dan kasuwa, Alhaji Ahmad Lawan Bichi ya gina da nufin yi wa mahaifinsa, Alhaji Lawan Mai Kanti, wanda ya rasu da jimawa, sadaka mai gudana, ya ce “na gina wannan makaranta don Allah, sannan don mahaifina da kuma koyi da fadar Hadisin Annabi (S.A.W.) cewa duk wanda ya rasu aikinsa na lada ya tsaya, sai dai wanda ya bar da nagari da yake yi masa addu’a ko kuma ya bar wani abin amfani ga jama’a”.
Alhaji Lawan ya kara da cewa tun farko an gina makarantar, mai ajujuwa shida, don karatun yaran da ba su wuce shekaru shida zuwa goma ba, “amma abin alfahari ne ganin har manya
suna nuna bukatar shiga makarantar, lamarin da wadanda makarantar ke hannunsu za su tsara yanda karatun zai gudana. Tuni dai an yi wa makarantar rijista, domin karatunta ya dace bai daya da wanda hukuma ta tsara wa makarantu a jihar”. Inji shi.
A halin yanzu dai an fara makarantar da yawan dalibai dari hudu ne, kuma shi zai ci gaba da daukar nauyinta kafin jama’a su shigo su karbe shi.
Alhaji Lawan ya yi kira ga masu hali da su rika aiwatar da abubuwan alheri domin jama’a, musamman ma wajen gina irin wadannan makarantu na al’umma, “domin abubuwa sun yi wa
gwamnati yawa, don haka ba za a tsaya ana jiran sai ta yi wa mutane komai ba”.
Tun farko a jawabinsa, jagoran taron, Sheikh Falalu yabawa ya yi da kwazon Alhaji Lawan tare da yi masa kyakkyawan fatan Allah Ya karba masa kyawawan ayyukansa, sannan kuma Ya sada ladar manufar ginin makarantar ga mahaifinsa, kamar yanda ya kudurta.