An kaddamar da sabuwar Rundunar Yaki da ’yan fashi a Gombe
A karshen makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta kaddamar da sabuwar rundunar yaki da ’yan fashi da makami mai suna F-SARS (Federal Special Anti Robbery Skuad) don yaki da miyagu da kuma ’yan fashi da makami.Da yake kaddamar da rundunar a hedkwatar ’yan sandan jihar da ke Gombe, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar […]
A karshen makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta kaddamar da sabuwar rundunar yaki da ’yan fashi da makami mai suna F-SARS (Federal Special Anti Robbery Skuad) don yaki da miyagu da kuma ’yan fashi da makami.
Da yake kaddamar da rundunar a hedkwatar ’yan sandan jihar da ke Gombe, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Austin Iwar, cewa ya yi kaddamar da sabuwar rundunar umarni ne daga Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya, Mista Solomon Arase.
Mista Austin Iwar, ya ce dama akwai rundunar yaki da ’yan fashi da makami mai suna SARS, a jihohi amma yanzu Babban Sufeton ya ce a bullo da ta kasa F-SARS, wadda za ta kara taimakawa don ganin a kawar da ta’addancin ’yan fashi a ko’ina a fadin kasar nan.
Kwamishinan ’Yan sandan ya ce bayan da aka bullo da sabuwar rundunar an sake musu yunifom na musammam da za su gane kansu a lokacin da suke bakin aiki, kuma su kadai ne suke da irin wannan yunifom.
Ya ce batun kayan aiki kuma ba matsala ba ne domin an ba su isassun bindigogi kirar AK47 da harsasai kwanso bibbiyu masu daukar guda 60 kownnensu ga kuma tiyagas da mota kuma suna da inshorar lafiya.
Ya yi wa al’ummar jihar albishir cewa su kwanta idonsu rufe za a kare musu rayuka da dukiyoyinsu, domin jami’ansa za su yi aiki tukuru don kawar da ’yan fashi da makami a fadin jihar.