An kaddamar da sayar da takin zamani ga manoma a Jihar Nasarawa
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta kashe sama da Naira miliyan 500 wajen sayo takin zamani domin amfanin manoman jihar Gwamna Umar Tanko Almakura ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da sayar da taki ton 4,500 da sauran kayayyakin aikin noma a kamfanin sarrafa takin zamani da ke kan hanyar Makurdi a ranar Alhamis. Gwamna Almakura […]

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta kashe sama da Naira miliyan 500 wajen sayo takin zamani domin amfanin manoman jihar Gwamna Umar Tanko Almakura ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da sayar da taki ton 4,500 da sauran kayayyakin aikin noma a kamfanin sarrafa takin zamani da ke kan hanyar Makurdi a ranar Alhamis.
Gwamna Almakura ya ce wannan yunkuri na daga cikin kokarin gwamnatinsa na inganta jihar tare da kyautata wa manoma. Shiri, wanda aka yi wa lakanin “A koma gona”, ya zo daidai, “Idan aka yi la’akari da harkar noma a matsayin babbar sana’a a jihar, shi ya sa ma gwamanati ta dauki wasu kwararran matakai na kyautata rayuwar manoma wajen samar musu kayayyakin amfanin gona. Gwamnati ta yi kyakkyawan tanadin taraktoci don taimaka wa matsakaitan manoma”. Inji shi.
Gwamna ya koka kan tafiyar hawainiya da gwamnatin tarayya ke yi wajen samar da tallafi ga manoma a kasar nan, lamarin da ya sa gwamnatinsa ta kashe makudan kudaden domin samar da takin zamani da sauran kayayyakin amfanin gona a daminar bana don morar manoma, kuma za a sayar da takin ne a kan farashi mai rahusa.
Tun farko kwamishinan gona da albarkatun ruwa, Mista Samuel Meshi ya jinjina wa gwamnan kan kokarinsa na farfado da fannin noma a jihar, shirin da zai taimaka wa manoma a jiha. Jim kadan bayan taron, Aminiya ta ji ra’ayoyin wasu manoma, inda ta fara da shugaban masu noman doya na jihar, Malam Adamu Madaki, wanda aka fi sani da “Doya 50” inda ya bayyana dacewar sayar da takin a kan lokaci, sai dai ya nuna damuwarsa dangane da karin kudi da aka samu, wanda zai yi kananan manoma matukar wahala wajen saye.
Shi ma shugaban manoman jihar, Alhaji Aliyu Usman kodayake ya yaba wa kokarin gwamnatin jihar na samar da takin bana cikin lokaci, ya yi kiran ta sake duba farashi don ba wa kananan manoma damar sayen takin. Daga nan sai ya shawarci manoma su yi amfani da takin yadda ya kamata.