An kaddamar da shirin bai wa manoma bashin taki a Jigawa

A ranar Litinin da ta gabata ce Our Family Farm suka kaddamar da kamfanin takin zamani na Fursa Fertilizer Company tare da kaddamar da rabon bashin takin ga manona a garuruwan Hadejia da Kafin Hausa da Kirikasamma da ke Jihar Jigawa

An kaddamar da shirin bai wa manoma bashin taki a Jigawa

A ranar Litinin da ta gabata ce Our Family Farm suka kaddamar da kamfanin takin zamani na Fursa Fertilizer Company tare da kaddamar da rabon bashin takin ga manona a garuruwan Hadejia da Kafin Hausa da Kirikasamma da ke Jihar Jigawa.

Da yake jawabi a lokacin bikin kaddamar da shirin, Shugaban Kamfanin, Malam Ahmad Hussain ya ce, “Muna sa ran takin zai kara bunkasa harkar noma da magance yunwar da ake fama da ita da kuma samar da ayyukan yi a fadin Najeriya.”

Ya kara da cewa, “Yanzu haka mun bayar da tallafin kusan tan 350 a matsayin bashi ga kananan manoma da kuma masu sha’awar fara noma.”

Malam Ahmad ya ce takin zai rika zuwa wajen manoman kai tsaye.

Ya ce za su tabbatar sun shiga lungu da sakon jihar don ganin sun saukaka wa manoman da kuma wadatar da masu bukatar takin ba tare da an wahalar da su ba.

A karshe ya ce sun saukaka matuka wajen biyan bashin takin da manoman suka karba, inda ya ce ba za su daura wa manoman nauyin kudi da ruwa ba.

Yunusa Bulama, manomi ne da ya samu tallafin, ya ce, “Hakika tallafin zai sa mu kara himma wajen noma, wanda daga haka muke sa ran zama masu bayarwa a nan gaba muma.”

A cikin wata wasika data samu sa hannun Ahmed Hussain, shugaban Kamfanin, ta ce, Kamfanin zai dinga gudanar da al’amuransa ne ba tare da an dorawa talakwa kudin ruwa ba.