An kaddamar da shirin bunkasa biranen Jihar Nasarawa
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya kaddamar da shirin tsara manyan biranen jihar da suka kunshi manyan garuruwa uku na jihar da suka hada da Lafiya da Keffi da Karu. Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya kaddamar da shirin ne a lokacin da Kamfanin ENbOCON CONSULTANT LIMITED ya gabatar masa da tsarin shirye-shiryen bunkasa biranen […]
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya kaddamar da shirin tsara manyan biranen jihar da suka kunshi manyan garuruwa uku na jihar da suka hada da Lafiya da Keffi da Karu.
Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya kaddamar da shirin ne a lokacin da Kamfanin ENbOCON CONSULTANT LIMITED ya gabatar masa da tsarin shirye-shiryen bunkasa biranen a gidan gwamnati da ke Lafiya.
Gwamna Al-Makura ya nuna farin ciki da gamsuwa kan wannan sabon tsarin tafiyar da al’amuran filaye wanda ya bayyana a matsayin mataki na karshe na shirin bunkasa birane na gwamnatinsa. Ya ba da tabbaci cewa matakin ba shakka shi ne babbar hanyar samar da ci gaba da ake bukata a jihar, inda ya ce don haka ne gwamnatinsa ta gayyato jami’an tuntuba da suke gudanar da al’amuransu daidai da zamani kan abin da ya shafi tafiyar da filaye da tsara manyan birane.
Gwamna Al-Makura ya yaba wa kamfanin dangane da samar da gundumomi a biranen Lafiya da Keffi da Karu kuma ya ce a kokarin gwamnatinsa na tabbatar da ingancin muhalli ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin duk mai yiwuwa don ganin an aiwatar da shirin bunkasa biranen jihar yadda ya kamata cikin lokac.
Ya gargadi masu hada-hadar filaye da masu yin gini ba bisa ka’ida ba a jihar su daina, domin duk wanda ya keta ka’ida ya kuka da kansa.
Tun farko a jawabin Manajan Shirin Kula da Filaye na Jihar Nasarawa (NAGIS) kuma daya daga cikin wadanda aka mika sunayensu ga Majalisar Dattawa domin nada shi minista Alhaji Ibrahim Usman Jibrin ya ce shirin ya hada da samar da wasu gundumomi da kuma shirin bunaasa garuruwan Keffi da Karu da kuma Lafiya. Ya yaba wa Gwamna Umaru Al-Makura kan kokarinsa na ganin ya kyautata yanayin muhalli don bunkasa biranen jihar.
Wakilin kamfanin ENbOCON CONSULTANT LIMITED da ya gabatar da tsarin, Mista Bulus Luka Ake ya ce akwai babban alfanu a cikin shirin da jihar za ta amfana da shi, musamman na samar da ci gaba da kuma karin kudin shiga.