An kaddamar da shirin tsabtace yankin Ogoni
A jiya ranar Alhamis ne aka kaddamar da shirin tsabtace yankin Ogoni da ke Jihar Ribas da ke fama da malalar gurbatar yanayi saboda malalar man fetur a yankin Neja-Delta.Matakin dai wani bangare ne na shawarar rahoton Hukumar Majalisar dinkin Duniya mai sa ido a kan muhalli, wanda aka gabatar a shekarar 2011.Sai dai Shugaba […]

A jiya ranar Alhamis ne aka kaddamar da shirin tsabtace yankin Ogoni da ke Jihar Ribas da ke fama da malalar gurbatar yanayi saboda malalar man fetur a yankin Neja-Delta.
Matakin dai wani bangare ne na shawarar rahoton Hukumar Majalisar dinkin Duniya mai sa ido a kan muhalli, wanda aka gabatar a shekarar 2011.
Sai dai Shugaba Muhammadu Buhari, wanda aka tsara zai kaddamar da shirin, bai halarci bikin ba, kuma babu wani dalili da aka bayar na rashin zuwansa, amma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilce shi.
A jawabinsa wanda Farfesa Osinbajo ya karanta Shugaban Buhari ya tuno da ziyarar da ya kai ne garin Bodo inda aka kaddamar da shirin a lokacin da yake Shugaban kasa na mulkin soja.
Shugaba Buhari ya bayyana kaddamar da shirin tsabtace yankin Ogoni da wani sabon babi ga yankin.
“Wannan aikin tabtacewar ba kawai ya tsaya ga tsabtace yankin ba ne, har ma ya hada da inganta dukiyaku da lafiyarku da sauransu,” inji Shugaba Buhari.
A jawabin Ministar Muhalli Hajiya Amina Mohammed ta nanata bukatar da ke akwai ta yin gaskiya da tuntubar juna wajen tsabtace yankin na Ogoni, inda ta ce: “Da gaske muke yi wajen gudanar da wannan aiki, kuma sauran sassan yankin Neja-Delta ma suna bukatar a tsabtace su.
A jawabin Shugaban Majalisar Sarakunan yankin Ogoni, Cif Mene Suanu TY Baridam ya shawrci shugabannin Najeriya ne su rika cika alkawuran da suka dauka ga jama’a. “Babu wata jikakka a tsakanina da Goodluck Jonathan… amma a wannan batu ya tafka kuskure,” inji basaraken.
Ya kara da cewa: “Duk da mun so mu ga Shugaban kasa hakn bai samu ba, mun gamsu da zuwanka (Mataimakin Shugaban kasa). Da kana nan a yau (Shugaban kasa) ba zaka ji damuwar komai ba, sai dai ka yi farin ciki. Muna bukatar a kara yi mana abubuwa a yankin Neja-Delta.
Sarkin Gokana King Ginniwa ya ce: “Babu zaman makoki a Ogoni, lokacin zaman makoki ya wuce. Mutane Ogoni suna murna. Ina godiya ga Shugaban kasa.”
Malalar mai a yankin Neja-Delta tana gurbata ruwan sha da lalata gonaki da kusan dukkan hanyoyin rayuwar mutanen yankin.
A farkon shekarar 2015 ne katafaren kamfanin mai na Shell ya dauki alhakin malalar mai mafi muni har sau biyu tare da biyan diyyar miliyoyin Naira ga al’ummar Bodo a yankin Neja-Delta.
Malalar man da aka samu a 1970 ita ce mafi muni da ta taba aukuwa a tarihin Najeriya tun bayan da aka gano man fetur a yankin na Neja-Delta a 1957, inda aka fara hakarsa a 1958.
Malalar man ta lalata kasar yankin, inda ta kashe kifaye da albarkatun kasa, kuma ta mayar da kasar yankin wacce ba za a iya noma a kanta ba.
A 1990 ne wadansu mutanen yankin Ogoni suka fara fafutikar neman ’yanci ga yankin, a karkashin jagorancin wani fitaccen marubuci mai rajin kare muhalli, marigayi Ken Saro-Wiwa.
Za a shafe shekara 25 zuwa 30 kafin a kammala aikin tsabtace yankin, kuma idan har gwamnati ta yi nasara, zai iya taimaka mata wurin samun karin goyon baya a yankin, abin da ka iya kaiwa ga rage tasirin kungiyoyin masu tayar da kayar-baya.