An kaddamar da shugabannin Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi
Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta kaddamar da sababbin shugabanninta da za su ja ragamar jam’iyyar har zuwa bayan zaben shekara ta 2015.Jam’iyyar ta kaddamar da shugabannin ne a karkashin sabon shugabanta da aka zaba wato Alhaji Uba Ahmed Nana da sakatarensa Barista Buhari Disina a ranar Litinin inda bikin ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar […]
Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta kaddamar da sababbin shugabanninta da za su ja ragamar jam’iyyar har zuwa bayan zaben shekara ta 2015.
Jam’iyyar ta kaddamar da shugabannin ne a karkashin sabon shugabanta da aka zaba wato Alhaji Uba Ahmed Nana da sakatarensa Barista Buhari Disina a ranar Litinin inda bikin ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar na jihar da wasu shugabanninta na kasa.
A jawbin sakataren riko na jam’iyyar Dokta danjuma Adamu Dabo ya yaba goyon bayan da ’ya’yan jam’iyyar suka ba su, kuma ya bukaci a ba sababbin shugabannin goyon baya don kai ta tudun mun tsira a zaben badi.
Uban Jam’iyyar Dokta Ibrahim Yakubu Lame tsohon Ministan ’Yan sanda ya gode wa ’ya’yan jam’iyyar kan goyon bayan da suka ba su har aka zabi sababbin shugabannin. Ya bayyana kudirinsa na fitowa takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC domin samar da sabon sauyi a jihar da kasa baki daya. Ya bayyana cewa gwamnatin PDP ba za ta iya magance matsalolin da suka addabi kasar nan ba, don haka ya zamo wajibi mutane su himmatu wajen ganin an samar da sauyi domin ciyar da kasa gaba tare da inganta tsaron jama’a da dukiyarsu da kare martabarsu.
An samu halartar manyan ’yan siyasa masu ra’ayin sauyi, irin su Barista Ibrahim Zailani da Sanata Sulaiman Nazif da Alhaji Kawu Labaran da Alhaji Ali Wakili da Dokta Ibrahim Yakubu Lame da sauransu, inda Barden Gabas na Bauchi Alhaji Shehu Aliyu Musa ya bayar da kyautar mota ga jam’iyyar.