An kaddamar da yaki da cututtukan amfanin gona
Gwamnatin Tarayya ta bayyana yunkurinta na yaki da kwari da sauran cututtukan da suke addabar kayan amfanin gona da nufin dakile karancin abinci a fadin kasar nan. Yayin da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar kan shekarar lafiyar tsirrai ta duniya ta shekarar 2020 ‘International Year of Plant Health, 2020’, Babban Daraktan Hada-Hadar […]
Gwamnatin Tarayya ta bayyana yunkurinta na yaki da kwari da sauran cututtukan da suke addabar kayan amfanin gona da nufin dakile karancin abinci a fadin kasar nan.
Yayin da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar kan shekarar lafiyar tsirrai ta duniya ta shekarar 2020 ‘International Year of Plant Health, 2020’, Babban Daraktan Hada-Hadar Kayan Amfanin Gona na Najeriya Dokta Bincent I. Isegbe ya ce, kwari da sauran cututtuka na bata kayayyakin da ake nomawa tare da janyo karancinsa a cikin kasar nan.
Isegbe, ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda cututtukan kan lalata kayan amfanin gona wanda hakan ke haifar da karancin abinci tare da hauhawar farashinsu a cikin kasuwa da kuma rashin tsayayyen farashi a kasuwanni da kamfanoni.
“Ana hasashen adadin ’yan Najeriya zai kai kimanin mutum miliyan 236 zuwa nan da shekarar 2030 yayin da adadin zai haura zuwa miliyan 410 zuwa shekarar 2050, wanda hakan ke nuna Najeriya za ta kasance daya daga cikin kasashe mafi yawan jama’a a duniya, kuma hakan yana nuna idan ba mu dauki matakin gaggawa don karfafawa tare da magance matsalolin da karuwar jama’a ba hakan zai iya haifar da karancin abinci. Abin da ya fi dacewa da mu yanzu shi ne inganta hanyoyin da za mu dogara da su wajen ciyar da kanmu kuma cikin sauri kafin nan da shekarar 2050 wanda rashin yin hakan ka iya haifar mana da matsalar fama da karancin abinci.” ya yi gargadi.
Ya ce, ciwo guda daya kawai na iya haifar da lalacewar abinci, inda ya tunatar da ’yan Najeriya irin yadda da cutar Ebola ta tumatir ta lalata tumatir mai yawa da manoman kasar nan suka noma a shekarar 2017 abin da ya janyo wa manoma asara mai yawa tare da haifar da gagarumin tashin farashin tumatir a kasuwannin Najeriya.
Isegbe ya bayyana tsarin da za su fito da shi da manoma za su yi amfani da shi a kasar nan wurin amfani da magungunan feshi don kare abin da aka noma daga kamuwa da wadannan cututtuka.