An kaddamar littattafai biyu kan Najeriya a Kaduna

A kwanakin baya ne aka kaddamar da wasu littattafai biyu kan Najeriya a Gidan Arewa da ke Kaduna, wadanda Abdulaziz A. Musa ya rubuta.Littattafan biyu masu taken ‘Nigeria: The Need for a Rebolution’ da kuma ‘100 kuestions for Nigeria at 100,’ an rubuta su ne da harshen Ingilishi. Marubucin ya bayyana cewa dalilin da ya […]

An kaddamar littattafai biyu kan Najeriya a Kaduna
An kaddamar littattafai biyu kan Najeriya a Kaduna

A kwanakin baya ne aka kaddamar da wasu littattafai biyu kan Najeriya a Gidan Arewa da ke Kaduna, wadanda Abdulaziz A. Musa ya rubuta.
Littattafan biyu masu taken ‘Nigeria: The Need for a Rebolution’ da kuma ‘100 kuestions for Nigeria at 100,’ an rubuta su ne da harshen Ingilishi. Marubucin ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya rubuta littattafan bai rasa nasaba da halin da kasar nan ke ciki ba, kamar tabarbarewar tsaro da rashin ayyukan yi da matsalolin rashin hadin kai tsakanin ’yan Najeriya da dai sauransu.
Ya kara da cewa: “Idan muna so kasar nan ta ci gaba, to sai mun warware wadannan matsalolin kuma su ne littattafan biyu ke magana a kai.” Inji shi.
Littafin 100 kuestions, yana Magana ne kan kalubalen da suka yi wa kasar nan dabaibayi. Ya kuma ba da haske kan hanyoyin da ’yan Najeriya za su bi don kawo karshen matsalolin da ke ci masu tuwo a kwarya.
Littafi na biyu kuwa yana ankarar da ’yan Najeriya ne bisa dacewar juyin-juya-hali, saboda halin da kasar ta samu kanta a ciki. Amma marubucin ya ce hakan na iya faruwa ba tare da daukar makami, ko yin fito-na-fito da mahukunta ba.
Babban Bako Mai kaddamarwa, Alhaji Sumaila Isa Funtuwa ya sayi littattafan biyu a kan Naira miliyan daya. Sai Shugaban Majalisar Wakilai, Alhaji Aminu Tambuwal, wanda dan Majalisa Garba Baba Datti wa wakilta, shi ma ya saye su a kan Naira miliyan daya.
Bikin ya kuma samu halartar manyan baki kamar su tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa da tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, James Bawa Magaji da Farfesa Ango Abdullahi da sauransu.