An kafa Amotekun don a tsangwame mu – Fulani Makiyaya

Kungiyar Fulani makiyaya ta Jamunatil Fulbe ta Fulani makiyaya ’yan kasa da ke zaune a jihohin Yamma da Jihar Kwara da ke da hedkwata a Jihar Oyo ta shirya taro a kauyen Bale da ke Karamar Hukumar Atiba a Jihar Oyo a ranar Asabar da ta gabata, inda shugabannin kungiyar suka bayyana cewa ba sa […]

An kafa Amotekun don a tsangwame mu – Fulani Makiyaya

Kungiyar Fulani makiyaya ta Jamunatil Fulbe ta Fulani makiyaya ’yan kasa da ke zaune a jihohin Yamma da Jihar Kwara da ke da hedkwata a Jihar Oyo ta shirya taro a kauyen Bale da ke Karamar Hukumar Atiba a Jihar Oyo a ranar Asabar da ta gabata, inda shugabannin kungiyar suka bayyana cewa ba sa shakkar rundunar tsaro ta Amotekun da gwamnonin jihohin Yamma suka kaddamar.                                                                                                                                          Shugabannin Kungiyar Jamunatil Fulbe sun ce su ma ’yan kasa ne da suke rayuwa a yankin tun iyaye da kakanni, don haka babu wani abin da zai zo cikin dan lokaci ya tayar musu da hankali.

Magatakardar Kungiyar Malam Abdullahi Salihu, ya shaida wa Aminiya cewa Fulani makiyaya da ke karkashin kungiyarsu ba su san ko’ina ba sai inda suke zaune a Kurmi, inda ya ce a fahimtarsu wadanda suka kirkiro kungiyar tsaro ta Amotekun sun yi haka ne domin su tsauwala wa Fulani makiyaya su samu damar tsangwamarsu, “Don haka mu Fulanin wannan yanki mun tabbata ba a kirkiri kungiyar Amoteku domin inganta tsaro ba an kirkire ta ce domin a muzguna mana wannan ne ya sa suke yawan ambatar kabilarmu kuma suka ware mu a tsarin, duk abin da aka ce an kafa domin a kalubalanci wadansu ko wata kabila ba a yi shi kan tsari ba. Domin ba a kabilar Fulani kadai ake da baragurbi, ko ’yan fashi ko masu garkuwa da mutane ba. Kuma mu ma al’ummar Fulani muna fama da matsalolin rashin tsaro lamarin da ya shafi masu satar shanu da masu garkuwa da mutane,” inji shi.

Ya ce an yi garkuwa da jama’arsu da dama wadansu sun biya kudin fansa sun fanshi kansu wadansu kuma an hallaka su. “Sannan akwai kalubalen da muke fuskanta  daga abokan zamanmu manoma a sassan  Jihar Oyo wadanda suke zuba guba a ruwan shan dabobbinmu ko su sa guba a roko su zubar a kan hanyar da dabobbinmu ke bi. Makiyayi ba zai ankara ba sai ya ga dabobbinsa na faduwa suna mutuwa. A irin haka mun rasa dabobbi sama da dubu uku daga bara zuwa bana a Jihar Oyo kadai,” inji shi.

Ya ce “Muna da tarin hotunan irin wadannan dabobbi da aka kashe mana mun kuma kai rahotanni da dama ga ’yan sanda, don haka mu ma al’ummar Fulani bai kamata a ware mu ba, domin muna bukatar tsaro, amma muddin aka kirkiri wani abu don a yake mu da shi ba a yi mana adalci ba.”

Ya ce ba sa goyon bayan sanya ’ya’ayn Kungiyar OPC a rundunar Amotekun domin a baya an kafa ta ce don ta yaki Fulani makiyaya mazauna jihohin Yamma da ragowar ’yan Arewa da ke zaune a yankin.

Malam Umar Abdulkadir Lamido ya shaida wa Aminiya cewa kamar yadda kowace al’umma ke bukatar tsaro haka su ma Fulani makiyaya ke bukatar tsaron rayukansu da dukiyoyinsu lura da yadda suke fuskantar kalubalen rashin tsaro, lamuran da suka shafi ta’asar barayin shanu da masu garkuwa da mutane da manoman da ke sanya wa dabobbi guba su ci su mutu.

Kakakin Kungiyar Malam Aliyu Modibbo ya shaida wa Aminiya cewa Fulani makiyaya da ke zaune a jihohin Yamma ba sa shakkar kungiyar tsaro ta Amotekun, inda ya ce Fulani da ke zaune a yankin sun riga sun zama daya da abokan zamansu Yarbawa, “Ni nan da ke magana da kai a Jihar Oyo aka haifi kakana, a nan aka haifi mahaifina shi kuma ya haife ne, sannan matata Bayarabiya ce ’yar wani basarake a Jihar Ondo. Haka jagoranmu na garin Isenyi Alhaji Yakubu Muhammad ya auri Bayarabiya ’yar Iseyin sannan Janhuranmu na garin Oke-Ogun ya auri Bayarabiyar Ilori. Don haka idan sun ga dama sun sanya mu cikin tsarinsu na Amotekun muna maraba da su idan kuma suka ce ba sa bukatarmu a ciki to su je su rike kayansu. Ba ma tsoronsu ko shakkarsu domin mu ma ’yan kasa ne tamkar kowa,” inji shi.

Garba Umaru, makiyayi a garin Iseyin cewa ya yi, akwai bukatar inganta tsaro, domin a halin da ake cikin jami’an tsaro sun gaza aikinsu na tsare dukiya da rayukan al’umma yadda ya kamata.

Fulanin sun bukaci a sanya su cikin shirin na Amotekun domin su bai wa al’ummarsu mazauna jihohin Yamma tsaro.

Sai dai a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta ki amincewa da kungiyar ta Amotekun masu goyon bayan tsarin sun gabatar da zanga-zanga a wasu daga cikin jihohin Kudu maso Yamma.