An kafa dokar auren mata da yawa a kasar Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sanya hannu a wata doka da za ta baiwa maza izinin auren mace fiye da daya a kasar.Dokar ta samu goyon bayan yawancin mazan da ke Majalisar kasar. Amma dokar ba ta samu karbu wa ga mata ‘yan majalisar. A al’adar mutane kasar dai, sai da amincewar matar da […]

An kafa dokar auren mata da yawa a kasar Kenya
An kafa dokar auren mata da yawa a kasar Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sanya hannu a wata doka da za ta baiwa maza izinin auren mace fiye da daya a kasar.
Dokar ta samu goyon bayan yawancin mazan da ke Majalisar kasar. Amma dokar ba ta samu karbu wa ga mata ‘yan majalisar. A al’adar mutane kasar dai, sai da amincewar matar da ke gida miji ke iya kara aure. Hakazalika, dokar na shan suka daga kungiyoyin addinnin Kirista da kuma kungiyoyin mata da ke kasar.
A watan jiya ne dai Majalisar Dokokin Kenya ta zartar da dokar wacce aka yi kan tsarin gargajiya. Sai dai ko a lokacin zartar da dokar mata ‘yan majalisar sun kaurace wa zaman majalisar bayan wata zazzafar mahawara da takwarorinsu maza kan batun.
Shugabannin Kristoci sun bayyana sanya hannun da Shugaba Kenyatta ya yi ga dokar  da  rashin daraja tanade-tanaden da addinin Krista kan aure da zaman takewar iyali. kungiyar Mata Lauyoyi a kasar, ta ce ba ta goyi bayan dokar ba kuma za ta kalubalanci hakan a gaban kuliya.