An kafa dokar hana fita a Unguwanni 5 na Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abubakar ya sanya dokar hana fita a Unguwanni biyar bayan wani rikici da faru tsakanin matasa akan budurwa lokacin bikin cika shekara wanda aka yi ranar daren Lahadi. Unguwannin da aka kafa dokar sun hada da: Yelwa Tsakani, Lushi, Unguwar Kusu, Unguwar Ngas da kuma Kagadama. Gwamnan jihar ne ya bayyana […]
Gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abubakar ya sanya dokar hana fita a Unguwanni biyar bayan wani rikici da faru tsakanin matasa akan budurwa lokacin bikin cika shekara wanda aka yi ranar daren Lahadi.
Unguwannin da aka kafa dokar sun hada da: Yelwa Tsakani, Lushi, Unguwar Kusu, Unguwar Ngas da kuma Kagadama.
Gwamnan jihar ne ya bayyana wa manema labarai hakan. Ya ce an kafa dokar ne saboda guje wa yaduwar rikicin a wasu yankunan jihar, dokar zata fara ne daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.