An kafa dokar hana fita bayan harin barikin soji da fasa gidan yari a Saliyo

Wasu mahara ɗauke da makamai sun fasa gidan yarin ‘Pademba Road’ da ke tsakiyar birnin Freetown.

An kafa dokar hana fita bayan harin barikin soji da fasa gidan yari a Saliyo

Yadda sojoji suke kokari tabbatar da dokar hana fita a Saliyo

Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita a fadin kasar sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai rumbun ajiye makamai da ke barikin sojin Freetown, abinda ya haifar da musayar wuta.

Shaidun gani da ido sun shiada wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewar, sun ji karar harbe harbe da kuma fashewar wani abu mai karfi a yankin Wilberforce, inda rumbun ajiye makaman yake, kusa da ofisoshin jakadancin kasashen ketare.

Wasu shaidun sun ce sun ji karar musayar wuta kusa da barikin sojin da ke unguwar Murray Town, da ke dauke da sansanin sojin ruwan kasar da kuma wani sansanin sojin da ke wani bangare na Freetown.

Wani faifan bidiyon da aka sanya a kafofin sada zumunta ya nuna wasu mutane a kan titunan kasar da aka ce sun gudu ne daga gidan yari bayan harin, amma Kamfanin Dillancin Labaran Faransa bai iya tantance wanda ya bude musu kofar fita ba.

Rahotanni sun ce an yi amfani da manyan makamai masu sarrafa kansu da kuma fashe fashe masu karfi kamar yadda aka dinga yadawa a kafofin sada zumunta.

Shaidun sun ce wannan ya sa mutane suka kauracewa titunan birnin Freetown domin komawa cikin gidajensu don kare lafiyarsu.

Wani jami’in da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce shaidun gani da ido sun tabbatar masa cewa wasu mahara ɗauke da makamai sun fasa gidan yarin ‘Pademba Road’ da ke tsakiyar birnin Freetown tare da sakin fursunoni.

Kawo yanzu ba a sa adadin fursunonin da suka tsere ba, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Wata da ake kira Susan Kargbo ta ce karar bindigogi da fashe fashen da taji ne daga barikin sojin Wilberforce suka tashe ta daga barci da misalin karfe 4.30 na safiyar yau.

Kargbo tace ta kadu sosai, yayin da harbe harben suka ci gaba har zuwa wayewar garin yau Lahadi.

Sanarwar gwamnati ta ce sojoji sun yi nasarar murkushe wadanda suka yi kokarin fasa rumbun ajiye makaman, yayin da aka bukaci jama’a su zauna a cikin gidajen su.

Ministan Yada Labarai, Chemor Bah ya shaida wa jama’a cewar gwamnati da kuma rundunar sojin kasar sun tashi tsaye wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu, yayin da ya kara da cewa domin bai wa jami’an tsaro damar farautar ‘yan bindigar da suka kai harin, an umurci jama’a da su zauna a gidajensu, yayin da aka saka dokar hana fita.

Babu wani karin haske a kan wadanda suka kai harin da kuma dalilin daukar matakin.

Yankin Afirka ta Yamma na fuskantar matsalolin juyin mulki tun daga watan Agustan shekarar 2020, ganin yadda kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar da kuma Guinea wadda ke da iyaka da Saliyo suka gamu da juyin mulkin soji.

Shugaban Kasar Saliyo Juluis Maada Bio ya bi sahun jami’an gwamnatinsa wajen kwantar da hankalin jama’a cewar hankali ya kwanta a birnin Freetown, tare da bukatar mutane su zauna cikin gidajensu.

Bio ya ce yayin da hadin gwuiwar hukumomin tsaron kasar ke farautar wadanda suka kai harin, an kafa dokar hana fita a kasar baki daya, tare da bukatar ganin jama’a sun zauna cikin gidajensu.

Shugaban ya sake jaddada cewar gwamnati zata ci gaba da samar da tsaro da kuma kare lafiyar al’ummar kasar daga barazanarwadanda basa son zaman lafiya.

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Freetown ya yi Allah wadai da yunkurin kai hari rumbun ajiye makaman, yayin da ya sha alwashin taimakawa wajen aiki da dimokiradiya da kuma zaman lafiyar Saliyo.

An dai zabi shugaba Maada Bio ne a shekarar 2018, yayin da a watan Yunin bana ya samu nasarar wa’adi na biyu da kuri’u sama da kashi 56 da aka kada.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja