An kafa dokar hana kiwo ne don tabbatar da zaman lafiya – Gwamnatin Benuwai

A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin Jihar Benuwai ta kafa dokar hana kiwo a jihar inda gwamnati ta tabbatar da dokar. Fulani makiyaya da dokar ta shafa sun yi ta korafin cewa gwamnatin ta kafa dokar ce domin ta kore su daga jihar baki daya kamar yadda ke kunshe a wata sanarwa da suka raba […]

An kafa dokar hana kiwo ne don tabbatar da zaman lafiya – Gwamnatin Benuwai

A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin Jihar Benuwai ta kafa dokar hana kiwo a jihar inda gwamnati ta tabbatar da dokar. Fulani makiyaya da dokar ta shafa sun yi ta korafin cewa gwamnatin ta kafa dokar ce domin ta kore su daga jihar baki daya kamar yadda ke kunshe a wata sanarwa da suka raba wa manema labarai a Lafiya fadar Jihar Nasarawa inda galibinsu suka dawo da dabbobinsu. Wakilinmu ya tattauna da Babban Sakataren Labarai na Gwamnan Benuwai, Mista Terbe Akase ta waya a kan lamarin inda ya ce an kafa dokar ce don tabbatar da zaman lafiya, kuma gwamnatin jihar ba za ta samar wa wadanda dokar ta shafa wuraren kiwo ba da sauransu: 

 

Al’ummar Fulani makiyaya a Jihar Benuwai ta bakin kungiyar Miyetti Allah sun soki dokar hana kiwo a fili da gwamnatin Samuel Ortom ta kafa a jihar wadda ta fara aiki kwanakin baya suna cewa ta kafa dokar ce don ta kore su daga jihar, me za ka ce?

Kafin in amsa wannan tambaya bari in tambaye ka, shin an taba kafa doka don a musguna ko a kori wani daga wani wuri? Ina so in bayyana maka cewa wadannan zarge-zarge ne da ba su da toshe don dokar hana kowo a fili doka ne da kafin Majalisar Dokoki ta fara zama a kanta ta zo Gwamna Samuel Ortom ya sa hannu ta zama doka sai da aka gayyaci jama’a daban-daban daga shiyyoyin jihar da shugabannin al’ummomi daga fannonin rayuwa don a ji ra’ayinsu. Kuma ina tabbatar har Fulani makiyaya da ke korafin da shugabanninsu duk an gayyato su, inda duk suka amince da wannan kudiri na gwamnati. Idan ba sa son dokar don wasu dalilai ya kamata su bayyana korafinsu a lokacin. Amma ba su yi haka ba sai yanzu da dokar ta fara aiki suke korafin cewa an kafa ta ce don a musguna musu ko a kore su daga Jihar Benuwai. A gaskiya idan sun yi haka ba su yi wa kansu da gwamnatin Ortom adalci ba. Kuma bayan gayyatar jama’a don a ji ra’ayinsu a kan dokar, gwamnati ta sanar da wannan kudiri a kafafen watsa labarai a ciki da wajen jihar da suka hada da rediyo da talabijin da jaridu inda ta bayyana alfanu da ke tattare da dokar da dalilan kafa ta. Sau da yawa idan kana sauraren bayyanan Gwamna Samuel Ortom a kan maganar rigingimun manoma da Fulani makiyaya da suka ki cinyewa a Jihar Benuwai da kasar nan baki daya za ka ji yana nanata cewa babbar hanyar da za a bi a iya rage ko magance lamarin kwata-kwata ita ce a kafa dokar hana kiwo a fili ko in ce ba bisa ka’ida ba. Shi ya sa tunda ya hau ragamar mulki ya yi ta yin duk mai yiwuwa don tabbatar an kafa dokar kuma ya yi ne don a samu dauwamammen zaman lafiya a tsakanin al’ummomin biyu a jihar da kasa baki daya. Kuma gwamnatin Ortom tana daya daga cikin gwamnatotin jihohin kasar nan da suke kashe makudan kudi wajen magance rigirgimun manoma da makiyaya kuma haka ba ci gaba ba ne don kudade ne da ya kamata a yi amfani da su wajen samar da kayayyakin inganta rayuwa ga jama’a, amma sai ya kasance ana ta kashewa a wajen tsaro. Kuma ya zame wa gwamnati dole ta yi don idan ba ta yi ba al’ummar jihar nan za su ci gaba da rasa rayuka da dukiyoyinsu. Kuma a yanzu mun gode Allah don a cikin mako biyu kacal da dokar ta fara aiki mun ga alamun dawowar zaman lafiya a jiharmu ta Benuwai kuma al’ummarmu a birane da kauyuka suna murna suna kuma yaba wa Gwamna Ortom da Majalisar Dokoki a kan wannan namijin kokari da suka yi. 

Saboda haka batun cewa an kafa dokar ce don a musguna wa Fulani ko a kore su daga Benuwai ba gaskiya ba ne, zargi ne da ba ya da tushe kamar yadda na bayyana a baya. Kuma ko kana sane cewa akwai ’yan asalin Jihar Benuwai da suke da dabbobi da suke kiwo a jihar? Ba Fulani ne kawai suke da shanu da sauran dabbobi suna kiwo a jihar ba, akwai kabilun jihar da dama da suka hada da Idoma da Agatu da Tibi da Igede da sauransu da suke da dabbobi suna kiwo kuma wannan doka ta shafe su. Saboda haka ba wai an kafa dokar saboda Fulani ne kawai ba har da sauran kabilun da suke da dabbobi. Ba a so a ga ana kiwo a ko’ina a jihar nan, kuma wannan doka ba sabuwar aba ba ce. Idan ka je kasar Indiya wadda ta fi mu arzikin shanu da sauran dabbobi ba za ka ga suna kiwo a duk inda da suka ga dama ba suna da tsari. Shi ya sa ba sa samun irin wadannan rigingimu na manoma da makiyaya. Haka lamarin yake a wasu kasashen duniya da dama.

Shugabannnin kungiyar Miyetti Allah reshin Jihar Benuwai sun fitar da sanarwa ga manema labarai a Lafiya, cewa lokacin da aka gayyaci mambobinsu don jin ra’ayinsu a kan dokar an yi jawabi ne da Ingilishi kuma ba a fassara musu ba. Hakan ya sa galibinsu ba su fahimci abin da ake nufi a wajen ba, me za ka ce?

Tambayar da zan yi maka da wane su Fulanin suka bayyana wannan sanarwa a Lafiya? Ba da Ingilishi ba ne? A bar wannan magana ma ai sau da yawa gwamnatin Benuwai takan gayyaci shugabanninsu a duk matakai duk lokacin da take son tattaunawa da su kan abubuwa da suka shafi al’ummarsu. Kuma na tabbata wadannan shugabanninsu suna isar musu da sakonnin har da wadanda ba sa jin Ingilishi. Saboda haka a ganina wadannan korafe-korafe marasa ma’ana ne kawai. Shawarar da zan ba su da sauran makiyaya da ke jihar ita ce su yi aiki da dokar, su kiyaye dokar don tabbatar da zaman lafiya musamman tsakaninsu da takwarorinsu manoma don samun ci gaba maidorewa a jihar nan baki daya.

Har ila yau Fulanin da lamarin ya shafa suna korafin cewa gwamnatin Benuwai ta kafa dokar ce ba tare da ta samar musu da wuraren kiwo a jihar ba. Yaya gaskiyar lamarin?

To da farko dai ina so in bayyana ko in sanar da kai cewa ba hakkin gwamnatin jihar nan ne ta samar wa wadanda dokar ta shafa wurare ko filin kiwo ba. Hakan yana bayyane a shafuka na 2 da 3 da 4 na kundin tsarin dokar inda aka bayyana cewa ba hakkin gwamnatin Jihar Benuwai ce ta samar wa makiyaya a jihar filayen kiwo ba. Sai dai dokar ta ce duk makiyayin da ke da filinsa na kansa zai iya kebe shi ya ci gaba da kiwon dabbobinsa, wanda ba ya da fili zai iya shiryawa da wani mai fili su sasanta idan sun gama sai su je Ma’aikatar Gona da Raya Albarkatun kasa ta Jiha su sanar da ita. Bayan ma’aikatar ta bincika ta gano cewa lallai filin nasa ne sai ta sa hannu a yarjejeniya da za su yi wato kamar shekarun da makiyayin zai yi yana amfani da filin da sauransu ta kuma kasance a matsayin shaida a kan yarjejeniyar da sauransu ba wai gwamnati ne za ta samar masa da wajen kiwo ba. Yadda dokar ta bayyana ke nan kuma makiyayan duk suna da sanin haka. 

A karshe ina so in yi amfani da dama in yi kira na musamman ga al’ummar Fulani makiyaya da sauran makiyaya daga sauran kabilun jihar baki daya cewa su rungumi wannan doka su hada hannu da gwamnatin Samuel Ortom a kokarin da yake yi na samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar nan da kasa baki daya. Domin Gwamna Ortom mutum ne da babu ruwansa da nuna son kai ko wani abu makamancin haka. Abin da ya sa a gaba a kullum yake kuma ba shi fiffiko shi ne yadda za a samu zaman lafiya mai dorewa, musamman a tsakanin Fulani makiyaya da manoma kasancewar ana rasa rayuka da dukiyoyi sakamakon rigirgimun da suke yi a jihar.