An kafa kungiyar hada kan al’ummar Musulmi a Kurosriba
Lura da yadda kan Musulmi a duniya yake rarrabe ne ta hanyar mabambantan akidu da kuma dariku ne ya sanya na kafa kungiyar hada kan limamai da malamai ta Najeriya a Jihar Kurosriba.Manjo Kabiru Yakubu Sa’ad, babban limamin masallacin barikin soja, Brigade na 13 da ke Kalaba Jihar Kurosriba ne ya bayyana haka, yayin zantawarsu […]
Lura da yadda kan Musulmi a duniya yake rarrabe ne ta hanyar mabambantan akidu da kuma dariku ne ya sanya na kafa kungiyar hada kan limamai da malamai ta Najeriya a Jihar Kurosriba.
Manjo Kabiru Yakubu Sa’ad, babban limamin masallacin barikin soja, Brigade na 13 da ke Kalaba Jihar Kurosriba ne ya bayyana haka, yayin zantawarsu da Aminiya a Kalaba. Ya ci gaba da cewa: “Kuma duka a karkashin tuta daya muke ta kalmar shahada, na biyu kuma yanayin yadda muke zaune a nan Kurmi na ga cewa abubuwan da ake yi ba su dace ba. Mu ba mu da yawa, na ga bai dace ba a ce ba mu da yawan Musulmi a nan jihar, ya dace mu hada kanmu saboda rarrabar kamar yadda Allah Ya ce a cikin littafinSa mai tsarki sai karfinmu ya tafi ya kare. Sai naga akwai muhimmancin mu hada kai tun da ba yawa ne da mu ba kuma yawanci duk baki ne. Shi ya sa na yi tunani na ce bari in yi kokari in kafa kungiyar hada kan limamai da malamai. Kuma alhamdu lillahi, yaki ya yi nasara kungiyar ta kafu.”
Ko akwai wata matsala da aka fuskanta yayin kafa wannan kungiya, lura da cewa akwai mabambantan dariku da kuma akidu? Tambayar da Sheik Yakubu Sa’ad ya amsa da cewa: “Gaskiya saboda Allah ban fuskanci wata matsala ba, na samu hadin kai da goyaon baya daga dukkanin limamai da malamai na masallatan Jihar Kurosriba da na kirawo, domin wannan bukata wadansu ma limaman ban taba ganinsu ba amma suka amsa kirana. Masallacin izala ne na ga suna dan dari-dari da abun, suka ce sai sun sanar wa hedkwatarsu da ke Jos tukunna, sai na ga ba su amince ba tun da su komai za su yi sai sun dauki umarni daga wani wuri. Don haka sai na rabu da su amma sauran masallatan sun ba da hadin kai. Yanzu haka saboda karbuwa da kungiyar ta yi, ana gudanar da tafsiri tare da buda baki a kowane masallaci, kowace Lahadi kuma komai tare ake yi, babu nuna wani bambanci.
Da yake yin tsokaci game da irin ayyukan da kungiyar za ta rika yi, ya kara da cewa: “To, ka ga ayyuka da yawa, na farko ba hada kan limamai da malamai za ta tsaya ba, dukkanin wani Musulmi yana cikin wannan kungiyar, sannan a hankali muna dubawa wuraren da babu masallatai da Musulmi suke; muna daukar wa’azi muna zuwa ana yi. Kuma ana samun masu musulunta, wannan kungiya za ta gina har ma da cibiyar nazarin addinin Musulunci, inda duk wanda ya musulunta za a kawo shi wurin a tsugunar da shi, a karantar da shi addini, ya fahimci wani abu. Daga baya a ba shi dan wani abu ya kama sana’a. Sauran ayyukan su ne sasantawa tsakanin ma’aurata da kuma yin sulhu tsakanin Musulmi da sauran ayyuka irinsu.