An kafa Kwamitin Kula da ambaliya a Jigawa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kafa kwamitin mutum tara da zai sanya ido a kan matsalar ambaliyar ruwa da ta shafi jihar. Da yake rantsar da ’yan kwamitin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abdulkadir Fanini ya ce Gwamnan Jihar ne ya umarce su da su hanzarta samar da sahihan bayanai a kan irin asarar da aka samu, […]

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kafa kwamitin mutum tara da zai sanya ido a kan matsalar ambaliyar ruwa da ta shafi jihar.
Da yake rantsar da ’yan kwamitin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abdulkadir Fanini ya ce Gwamnan Jihar ne ya umarce su da su hanzarta samar da sahihan bayanai a kan irin asarar da aka samu, sakamakon ambaliyar da ta shafe gonaki da gidaje a fadin jihar. Ya kuma shawarci ’yan kwamitin su zama masu adalci wajen tattara bayanai kuma su guji rubuta bayanan son rai, kuma su tabbatar sun rubuta sunayen wadanda al’amarin ya shafa da irin agajin da suke bukata.
Kwamashinan Aikin Gona na Jihar, Malam Kabiru Ali ne Shugaban kwamitin.
A cikin wata takarda da Kakakin Shugaban Ma’aikata, Malam Isma’ila Dutse ya sanya wa hannu, ta bayyana sunayen sauran mambobin kwamitin, wadanda suka hada da wakilan Ma’aikatar Lafiya da ta Ilimi da ta Muhalli da ta Ayyuka da Gidaje da kuma Ma’aikatar kananan Hukumomi da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa.
Da yake mayar da jawabi, Shugaban Kwamitin Malam Kabiru Ali ya ce gwamnati ta lura da muhimmancinsu ne, shi ya sa ta dora masu nauyin, don haka ya yi fatan Allah Ya zame musu jagora.
Bincike ya nuna, yanzu haka sama da kananan hukumomi 13 ne matsalar ambaliyar ta shafa a jihar ta Jigawa.