An kafa na’urar gano magudin jarrabawa a Kwalejin Ilimi ta Nasarawa
An kaddamar da fara amfani da wata na’ura ta musamman da za ta rika gano daliban da ke magudin jarrabawa a Kwalejin Ilimi ta Jihar Nasarawa da ke Akwanga a Jihar Nasarawa. A jawabinsa a wajen kaddamarwar a harabar kwalejin a karshen mako, Kwamishinan Ilimi na Jihar Nasarawa, Alhaji Tijjani Ahmed ya bayyana cewa kafa […]
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu
An kaddamar da fara amfani da wata na’ura ta musamman da za ta rika gano daliban da ke magudin jarrabawa a Kwalejin Ilimi ta Jihar Nasarawa da ke Akwanga a Jihar Nasarawa. A jawabinsa a wajen kaddamarwar a harabar kwalejin a karshen mako, Kwamishinan Ilimi na Jihar Nasarawa, Alhaji Tijjani Ahmed ya bayyana cewa kafa na’urar a ajujuwan kwalejin ya zame wa gwamnati wajibi, domin magance yawan magudin jarrabawa da yanzu ya zama ruwan dare a kwalejoji da jami’o’in kasar nan.
Ya ci gaba da cewa “Bayan mun gano wadansu dalibai sun fito da sababbin dabarun magudin jarrabawa a yanzu da hakan ya sa galibin malamansu ba sa iya gano su a lokutan da suke satar jarrabawar. “Na tabbata dubun irin wadannan dalibai za ta cika a makarantun gwamnatin jihar nan ba da dadewa ba, sakamakon fara yin amfani da wadannan na’urori,” inji shi.
Ya bayyana takaicinsa game da yadda a cewarsa galibin daliban kwalejin da sauran manyan makarantun gwamnatin jihar maimakon su mai da hankalinsu wajen yin karatu tukuru sai su rika mantawa da abin da ya kai su makaranta, a karshe su rika magudin jarrabawa.
Ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Jihar da hadin kan mahukuntan kwalejin tuni suka tsara iren hukunci da duk dalibi ko dalibar da na’urar ta gano da aikata laifin zai fuskanta.
“Gwamnatin Jiha da Ma’aikatar Ilimi za su ci gaba da samar da na’urorin ga dukan manyan makarantunta nan ba da dadewa ba, don tabbatar da an cimma wannan buri da zai tabbatar da daliban suna mai da hankali a karatu maimakon satar jarrabawa, musamman ta amfani da wayar salula da sauransu.
Ya shawarci daliban manyan makarantun gwamnatin jihar su mai da hankali ga karantunsu, su kuma guji munanan dabi’u da shiga kungiyoyin asiri da sauransu.
A jawabin Shugaban Kwalejin, Dokta Rebecca Issac Umaru ta yaba wa gwamnatin jihar dangane da wannan mataki, inda ta tabbatar da cewa hukumar kwalejen za ta tabbatar an cimma burin kafa na’urorin a kwalejin, sannan ta shawarci daliban makarantar su bi doka.