An kafa rundunar kasashen Musulmi don yaki da ta’addanci

A ranar Talatar da ta gabata ne kasar Saudiyya ta sanar da kafa wata sabuwar rundunar sojojin kasashe 34 da akasari kasashen Musulmi ne domin yaki da ta’addanci.Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya (SPA), ya ce daga birnin Riyadh na Saudiyya za a rika tsara ayyukan dakarun kawancen.kasashen da ke cikin hadakar, sun fito ne daga […]

An kafa rundunar kasashen Musulmi don yaki da ta’addanci
An kafa rundunar kasashen Musulmi don yaki da ta’addanci

A ranar Talatar da ta gabata ne kasar Saudiyya ta sanar da kafa wata sabuwar rundunar sojojin kasashe 34 da akasari kasashen Musulmi ne domin yaki da ta’addanci.
Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya (SPA), ya ce daga birnin Riyadh na Saudiyya za a rika tsara ayyukan dakarun kawancen.
kasashen da ke cikin hadakar, sun fito ne daga yankunan Larabawa da Asiya ta Kudu da kuma Afirka ciki har da Najeriya.
Da yake magana a wajen wani taron manema labarai, Yarima Mohammed Bin Salman ya ce hadakar dakarun za ta yaki kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a kasashen Iraki da Siriya da Libya da Masar da kuma Afghanistan.
Sai dai babu cikakken bayani game da yadda hadakar za ta tunkari wannan yaki a zahiri.
kasashen Larabawa na yankin Gulf dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba a kan su kara hobbasa wajen yaki da kungiyar IS a Iraki da Syria.