An kafa tarihin sanya hijabi karon farko a Gasar Kofin Duniya ta Mata

Nouhaila Benzina ta zama ’yar wasa ta farko mai sa hijabi a Gasar Kofin Duniya ta Mata.

An kafa tarihin sanya hijabi karon farko a Gasar Kofin Duniya ta Mata

An kafa tarihi a Gasar Kwallon Kafar Mata ta Duniya ta FIFA a karon farko bayan da Nouhaila Benzina, ’yar wasa ta farko sanye da hijabi, ta buga kwallo a tawagar The Atlas Lionesses ta kasar Maroko.

Nouhaila Benzina ta zama ’yar wasa ta farko mai sa hijabi a Gasar Kofin Duniya ta Mata inda ta buga wa Maroko a fafatawarta da Jamus.

Sannan kuma wasan ne karon farko da wata tawagar matan Larabawa daga yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka take fafatawa.

Duk da cewa Jamus ta sha Maroko 6-0 a wasan da aka yi ranar Litinin a Filin Wasa na Melbourne, masoya kwallon kafa daga duniyar Larabawa na fatan tawagar za ta yunkuro a wasanta na gaba.

Benzina, mai shekara 25, wacce take kuma buga wa tawagar Rundunar Sojin Maroko FAR, ta fara wasa a tawagar kasar ne a shekarar 2018.

Gabanin nan, ’yar wasan bayan ta nuna bajintarta a yayin da take wasa a tawagar ’yan kasa da shekara 20 ta Maroko a shekarar 2017.

Kasancewarta a filin wasa ya ja hankali sosai saboda batun ba da damar sanya hijabi a yayin wasa.

Nouhaila ta zama wata abar misali ta jajircewa da saka himma ga mata Musulmai da suka shafe shekaru suna neman a daina kyamar Musulunci musamman haramcin da FIFA ta saka na sanya hijabi.

Haramcin da FIFA ta saka na sanya hijabi

Haramcin, wanda aka sanya shi har zuwa shekarar 2014, ya zama wani tarnaki ga mata da dama da ke muradin sa hijabi yayin wasanni a duniya.

Lamari na farko da ya faru dangane da haka shi ne na Asma Mansour a 2007, wacce aka hana ta yin wasan kwallon kafa a Quebec saboda ta saka hijabi.

Abubuwa irin haka da suka faru ne suka jawo fara fafutukar neman ’yancin saka hijabi yayin wasan kwallon kafa.

A shekarar 2014, FIFA ta dage haramcin da ta saka na amfani da hijabi. Wannan mataki ya zama wata gagarumar nasara ga Musulmai a kokarin da mata suka yi don ganin an saka su a harkar wasanni da suke tsananin so.

Yadda Faransa ta cire masu saka hijabi daga harkar kwallon kafa

Sai dai duk da sauyin tsarin da FIFA ta yi, Faransa da Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa (FFF) har yanzu ba sa barin mata masu sanye da hijabi su yi wasan kwallo.

Dokar mai cike da ce-ce-ku-ce da aka amince da ita a Faransa a 2004 ta haramta “amfani da duk wata alama ko kaya da ke nuna siyasa ko akidar falsafa da ta addini ko alaka da wata kungiya.” Hakan kuwa ya hada har da sanya hijabi a filin wasa.

A watan jiya, Babbar Kotun Faransa Le Conseil d’Etat, ta yanke hukunci daidai da muradin hukumar FFF na haramta amfani da duk wata alama ta addini, ko da kuwa ta takaita ‘yancin albarkacin baki.

Wannan hukunci ya yi hannun riga da tsarin FIFA, lamarin da ya jawo damuwa da rashin jin dadi ga mata Musulmai masu ra’ayin wasan kwallo kafa a Faransa.

Kungiyar Les Hijabeuses

Kungiyoyi irin su “Les Hijabeuses” sun yunkuro suna kalubalantar haramcin tare da fafutukar ganin an samu damar sanya a yayin wasan kwallon kafa.

Ta hanyar tattara ’yan kwallo masu son sanya hijabi 80 a Faransa, kungiyar Les Hijabeuses ta yi amfani da shafukan sa da zumunta da rubuta korafe-korafe da kuma samun goyon bayan al’umma, ciki har da kamfanin Nike, don gabatar da kukansu.

“Abin da muke so shi ne amince da mu a yadda muke, a yi amfani da taken nan da ake yi na rashin nuna wariya da kuma tafiya da kowa,” kamar yadda Founé Diawara, shugabar kungiyar Les Hijabeuses, ta shaida wa The New York Times.

“Babban muradinmu shi ne akwai mu yi wasan kwallon kafa.

Kungiyar ta samar wa matan Musulmai wata kariya don yin kwallon kafa, da hada kai da sauran bangarori da kuma karfafa wa matan Musulmai matasa gwiwa don rungumar wasanni.

Kasancewar Nouhaila Benzina a Gasar Kofin Duniya da ya zama tarihi, ba ci gaban da aka samu kawai ke nunawa ba, har ma da kara wa mata masu muradin sa hijabi yayin wasanni kwarin gwiwa.

Tasirinta ya wuce a filin wasan kawai, ya hada har da aika sako na karfafawa da wakilci da damawa da kowa.

“A yayin da ta sanya kafarta a filin wasan, nasarorin Nouhaila sun tuna mana cewa ana iya kawar da duk wani tarnaki tare da cimma burin rayuwa, ko da wace irin sutura mutum ya sanya.

“A ranar Litinin duniya ta shaidi wani gagarumin ci gaba a tarihin kwallon kafa – wani abu da ke nuna karfi da jajircewa da karfin hadin kai da kuma jin dadin yin wasan da dukkanmu muke so.”

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja