An kai hari makarantar mata da yin garkuwa da malamai a Zamfara
Wasu ‘Yan bindiga masu yin garkuwa da mutane sun kai hari a wata makarantar sakandare ta Mata a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da mutanen da dama. ‘Yan bindigar sun kai harin ne a makarantar sakandare ta mata a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi da dare lokacin ake kallon wasan zakarun […]
‘Yan bindigar sun kai harin ne a makarantar sakandare ta mata a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi da dare lokacin ake kallon wasan zakarun Turai, kamar yadda wani mazauni garin ya shaida wa majiyar BBC.
Ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta lokacin da suka shiga garin inda suka kashe wani mutum guda.
Wani dan sa-kai a garin na Moriki ya ce tun da la’asar ‘yan bindigar suka tare hanya kafin daga baya suka kawo hari da daddare.
Ya ce sun tafi da wasu malamai biyu da wasu mata hudu masu dafawa dalibai abinci, amma ba su yi nasarar isa inda daliban ke bacci ba.