An kai hari na 4 Ofishin INEC a Imo

Mahara sun sake kai hari a ofishin Hukumar zabe ta kasa (INEC) a Jihar Imo a karamar hukumar Isu hari.

An kai hari na 4 Ofishin INEC a Imo

Mahara sun kai sabon hari a ofishin Hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke Karamar Hukumar Isu ta Jihar Imo.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na INEC, Festus Okoye ya ce karo na hudu ke nan da aka kai irin harin a jihar, bayan na kananan hukumomin Orlu da Oru ta Yamma da hedikwatar INEC ta jihar da ke Owerri.

Ya ce Kwamishinar INEC ta jihar, Farfesa Sylvia Agu ta sanar da su cewa da safiyar Talata maharan suka farfasa tagogi takwas na ofishin, amma ba su samu nasarar haurawa ciki ba.

“Duk da haka, mun kwashe muhimman kayayyaki kamar akwatunan zabe zuwa wata cibiyar INEC saboda tsaro.

“Hakazalika, duk wasu katinan zabe na dindindin da masu su ba su karba ba, an adana su, sannan an jibge jami’an tsaro a wurin saboda tabbatar da mutane sun ci gaba da zuwa karba ba tare da wata matsala ba ,” in ji shi.

Okoye ya ce INEC ta kai rahoton harin ga ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin daukar matakin da ya dace.