An kai hari ofishin ’yan sanda wasu jami’ai sun mutu a Borno
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya (I-G), Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin kamo waɗanda suka kai harin nan take.
Aƙalla jami’an ‘yan sanda biyu ne suka mutu a lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai hari a hedikwatar ‘yan sanda reshen Nganzai da ke Jihar Borno, ranar Alhamis.
‘Yan ƙungiyar sun kai harin ne kwanaki kaɗan bayan sun kai hari a sansanin Sojoji a Borno, inda suka kashe sojoji da ba a tantance adadinsu ba.
- Kano: Na kusa tona asirin maciya amana —Bichi
- Sudan ta kaddamar da sauye-sauye a kundin tsarin mulki
Hedkwatar tsaron Ƙasa ta ce ta yi asarar jami’anta shida a harin da aka kai, amma ta kashe ‘yan tada ƙayar baya 34.
Sai dai a harin ofishin ‘yan sandan an kashe jami’an da aka bayyana sunayensu da sufeto Bartholomew Kalawa da Kofur Mustapha Huzaifat.
Da yake mayar da martani, Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya (I-G), Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin kamo waɗanda suka kai harin nan take.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Adejobi ya ce Sufeta Janar ya umarci mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda (AIG) mai kula da shiyya ta 15, Mista Kenechukwu Onwuemelie, da ya tattara isassun kayan aiki da jami’an da za su kamo waɗanda suka aikata laifin.
Ya ce AIG ɗin zai kuma haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin ganin an gano waɗanda suka aikata laifin tare da fuskantar hukunci.