An kai harin kunar bakin wake ranar Sallah a Yemen

Akalla sojojin kasar Yemen 10 ne suka mutu a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan wani sansanin dakarun tsaro kusa da filin jirgin sama na birnin Aden, mai tashar jiragen ruwa.Hakazalika, ‘yan bindiga sun dirarwa babbar hedkwatar tsaro a yankin Khormaksar, da ke Kudancin birnin Aden, inda suka bude wuta.Har zuwa […]

An kai harin kunar bakin wake ranar Sallah a Yemen
An kai harin kunar bakin wake ranar Sallah a Yemen

Akalla sojojin kasar Yemen 10 ne suka mutu a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan wani sansanin dakarun tsaro kusa da filin jirgin sama na birnin Aden, mai tashar jiragen ruwa.
Hakazalika, ‘yan bindiga sun dirarwa babbar hedkwatar tsaro a yankin Khormaksar, da ke Kudancin birnin Aden, inda suka bude wuta.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma kungiyoyin IS da al-kaeda sun sha kai irin wadannan hare-hare a baya.
Saudiyya da dakarun da ke goyon bayan gwamnati suna ta fafutukar ganin sun kwace iko da babban birnin kasar Sanaa daga hannun ‘yan tawayen Houthi.
A watsn jiya ne bangarorin da ke rikici da juna a kasar suka yi musayar fursunoni masu yawa da aka kama watannin da suka gabata a lokacin gwabza fada a tsakiyar birnin Taiz.
An saki kusan ‘yan kabilar Houthi 120, inda aka musanya su da mayakan da ke mara wa gwamnati baya guda 74.
Musayar fursunonin dai wani shiri ne da aka yi tsakanin ‘yan tawayen, kuma ba ya daga cikin bangaren tattaunawar zaman lafiya da ake yi a kasar Kuwait.