An kai mahaifiyar Rarara asibiti

Ana duba lafiyar mahaifyar Rarara a wani asibiti a Abuja bayar masu garkuwa da ita sun sako ta

An kai mahaifiyar Rarara asibiti

An kai mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara asibiti bayan ’yan bindiga da suka yi garkuwa da ita sun sako ta.

A  safiyar Laraba Mawakin da kansa ya sanar da labarin sako ta gami da wallafa hotonsa tare da ita bayan an sako ta.

A cikin bidiyon, Rarara ne zaune a kusa mahaifiyar tasa, yana rungume da ita in da ya bayyana godiyarsa ga Allah da kuma mutanen da suke taimaka da addu’o’i.

Kimanin kwana 20 ke nan bayan ’yan bindiga sun sace dattijuwar a gidanta da ke kauyen Kahutu a Karamar Hukumar Danja a Jihar Katsina.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Aminiya cewa an wuce da mahaifyar Rarara zuwa wani asibiti a Abuja.

Majiyarmu ta gano cewa mahaifiyar Rarara na fama da cutar hawan jini kafin a yi garkuwa da ita.

A cewarsa, rashin lafitar ta tsananta a lokacin da take hannun masu garkuwa da ita kafin su sako ta.

A ranar 28 ga watan Yuni, 2024, ’yan bindiga suka shiga gidan mahaifiyar Rarara suka sace ta inda daga bisani suka bukaci kudin fansa Naira miliyan 900.