An kai mummunan hari kan jirage ruwan yakin Rasha

Rasha ta zargi Ukraine da kai mummunan hari da jirage sama marasa matuka kan shalkwatar jiragen ruwan yakinta da ke garin Sevastopol da ke bakin gabar teku. A cewar jami’an Rasha, An soma kai harin ne da misalin karfe 4:20 agogon kasar a inda jiragen sama marasa matuka suka soma luguden wuta. Jirage marasa matukan […]

An kai mummunan hari kan jirage ruwan yakin Rasha

Jirgin saman Ukraine

Rasha ta zargi Ukraine da kai mummunan hari da jirage sama marasa matuka kan shalkwatar jiragen ruwan yakinta da ke garin Sevastopol da ke bakin gabar teku.

A cewar jami’an Rasha, An soma kai harin ne da misalin karfe 4:20 agogon kasar a inda jiragen sama marasa matuka suka soma luguden wuta.

Gwamnan yankin wanda Rasha ta nada, Mikhail Razvozhaev, ya ce, sojojin ruwan Rasha sun mayar da martanin harin, inda suka kakkabo jiragen saman marasa matuka.

A cewarsa, wannan hari shi ne mafi girma da aka kai wa Rasha a yankin tun lokacin da ta shiga yankin na Krimea a watan Fabrairu.

A harin an lalalata akalla jirgin ruwan yakin Rasha guda daya, sannan babu wani gini na farar hula da harin ya shafa.

Garin Sevastopol shi ne gari mafi girma a yankin Krimiya da Rasha ta kwace a hannun Ukraine a shekarar 2014.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos