An kai wa Gwamnan Binuwai hari

An yi kazamin fada tsakanin jami’an tsaron gwamnan da maharan.

An kai wa Gwamnan Binuwai hari

An kai wa ayarin motocin Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, harin kwanton bauna a ranar Asabar.

An kai wa gwamnan hari ne a kan hanyar zuwa Tyomu da ke Karamar Hukumar Makurdi, hedikwatar jihar.

Harin ya ritsa da Ortom ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Gboko zuwa Makurdi da misalin azahar.

Shaidu sun ce an yi kazamin fada tsakanin jami’an tsaron gwamnan da maharan a babbar hanyar Makurdi-Gboko.

A dakaci karin bayani.