An kai wa tawagar ’yan takaran Gwamnan Taraba hare-hare

An kai hari ga ayarin yakin neman zabe na dan takarar Gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar SDP Mista Dabid Kente a kauyen Suntai da ke karamar Hukumar Bali a kan hanyarsa ta komawa Jalingo bayan ya gudanar da kamfe a kananan hukumomi da ke Kudancin Jihar inda wasu gungun matasa da ake kyautata zaton […]

An kai wa tawagar ’yan takaran Gwamnan Taraba hare-hare
An kai wa tawagar ’yan takaran Gwamnan Taraba hare-hare

An kai hari ga ayarin yakin neman zabe na dan takarar Gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar SDP Mista Dabid Kente a kauyen Suntai da ke karamar Hukumar Bali a kan hanyarsa ta komawa Jalingo bayan ya gudanar da kamfe a kananan hukumomi da ke Kudancin Jihar inda wasu gungun matasa da ake kyautata zaton magoya bayan Jam’iyyar PDP ne suka far musu.

A lokacin farmakin an lalata motoci fiye da goma har da motar da dan takaran ke ciki, kuma an ji wa jama’a da dama rauni.
Garin Suntai nan ne mahaifar Gwamnan Jihar danbaba Suntai kuma ’yan tawagar da ke raka Mista Dabid Kente sun zargi wani babban dan siyasa na hannun daman danbaba Suntai ne ya kitsa kai harin.
Mista Dabid Kente ya ce wannan lamari ya ba shi mamaki domin wucewa tawagarsa take yi ta garin na Suntai sai kawai aka kai masu hari da manyan makamai.
Ya ce maharan sun yi ta sarar motarsa amma bas u sami nasarar yin masa rauni ba sai dai an lalata motar da kuma wasu motocin ayarinsa.
Mista Dabid Kente ya ce ya kammala kamfensa a kananan hukumomin Kurmi da Ussa da Takum lafiya amma isowarsu Suntai ke da wuya sai aka far musu.
A wata sabuwa kuma an yi wa tawagar kamfe na dan takarar Gwamnan Jihar Taraba a Jam’iyyar PDP Mista Darius Ishaku ruwan duwatsu ga garin Karim Lamido mahaifar Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi.