An kai wa unguwar Hausawa hari a Imo

Jami’an tsaro sun shafe tsawon daren Litinin zuwa wayewar garin Talata suna artabu da maharan

An kai wa unguwar Hausawa hari a Imo

’Yan bindiga sun kai hari da nufin kwace ikon wata unguwar Hausawa da ke garin Owerri, babban birnin Jihar Imo.

An wayi garin Talata da jin karar harbe-harbe a yankin Douglas Road da ke kwaryar garin na Owerri.

Shaidu sun ce an shafe tsawon daren Litinin zuwa wayewar garin Talata sojoji da jami’an ’yan sanda suna ba-ta-kashi tsakaninsu da ’yan bindigar.

Bidiyon harin da ke yawo a kafafen sada zumunin ya nuna mutane na ta guje-guje domin kauce wa yiwuwar a harbe su.

Bayan da jami’an tsaron suka dandana musu kudarsu, sai maharan suka cika bujensu da iska suka yi layar zana.

Hadimin Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo kan Harkokin Al’ummar Arewa da Masu Rauni, Sulaiman Ibrahim Sulaiman, ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da cewa jami’an tsaro sun fatattaki ’yan bindigar.

Wakilinmu ya yi kokarin tattaunawa da kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Imo, SP Orlando Ikeokwu, amma hakar ba ta cimma ruwa ba.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna